Abubuwan da kananan ’yan kasuwar Afirka ke bukata don bunkasa harkokinsu

Abubuwan da kananan ’yan kasuwar Afirka ke bukata don bunkasa harkokinsu

Bunkasar Afirka a nan gaba ta ta’allaka ne a kan ci gaban kasuwancin yankin.
Cikin matsalolin kananan 'yan kasuwa a Afirka har da karancin kwararrun masana gudanarwa da za su taimaka wajen habaka kasuwancin nahiyar. Hoto/Reuters

Daga Rashida Abdulai

Masu gudanar da kanana da matsakaitan masana’antu a Afirka ba sa jin dadin yanayin da suke ciki na gudanar da kasuwancinsu, musamman wadanda suke da burin bunkasa harkokinsu.

Kanana da matsakaitan kasuwanci - da aka fi sani da SME - su ne mafiya yawan kamfanoni a nahiyar Afirka, da ma duniya baki daya.

Su ne ginshikin tattalin arzikin duniya, inda suke samar da sama da kashi 80 na ayyukan yi a Afirka tare da zama gaba-gaba wajen samar da kudin shiga.

Wannan ne ya sa a zahiri ake cewa habaka bangaren saukaka wa masu zuba jari yana da matukar muhimmanci wajen samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin Afirka cikin gomman shekaru masu zuwa.

Bunkasar Afirka a nan gaba yana ta’allaka ne a kan ci gaban kasuwancin yankin, wanda ta nan ne za a tarbi karuwar hayayyafar da ake yi a yankin.

Nahiyar, mai kusan mutum biliyan 1.2, da sababbin kamfanoni da kuma tsarin rashin shingen kasuwanci a nahiyar na African Continental Free Trade Area (AfCFTA), na nuna cewa akwai damarmakin kasuwanci da dama a yankin.

Sai dai dubban masu kanana da matsakaitan kasuwancin na Afirka ba sa jin dadin yanayin da suke ciki na gudanar da kasuwancinsu, musamman ma wadanda suke da burin habaka.

Gudanar da ayyukansu ya yi tsauri da tsada saboda rashin ababen more rayuwa, wanda bai rasa nasaba da yadda yankin ya dade cikin rashin ci gaba musamman a bangaren sufuri da rashin wutar lantarki.

Sannan akwai karancin kwararrun masana gudanarwa da za su taimaka wajen habaka kasuwancin yankin. Ana bukatar jari domin magance wannan matsalar.

Amma yawancin kanana da matsakaita ’yan kasuwar suna samun tallafin kadan ne, wanda ya yi matukar kasa da abIn da suke bukata, sannan basukan banki suna da wahala musamman wajen ribar da bankunan da suke sakawa.

Hanyar cike wannan gibin shi ne sanya hannun jari daga masu zaman kansu da cibiyoyin tattalin arziki da hadakar zuba jari da hada hannu da manyan kamfanoni.

Haka kuma nasarar da saye da sayarwa ta hanyar intanet wato Fintech da ake samu, ya bude wani sabon babi na tara kudi da tsarin abokin hulda da abokin hulda wato peer-to-peer (P2P) da kamfanoni irinsu Auspicious Blockchain da ke hada masu zuba jari daga ’yan Afirka mazauna Turai, da ’yan kasuwa da suke harkokinsu a yankin.

Matsalar ita ce, a lokuta da dama akwai ‘rashin tsarin shari’a’ tsakanin masu zuba jarin da ’yan kasuwar na Afirka.

Amma a Strand Sahara, mun gano wasu kalubalen shara’a guda uku da kanana da matsakaitan masana'antun Afirka ke fuskantar.

Ba a girmama su

Matsalolin nan ba masu zuba jarin kadai za su kora ba, har kasuwancin baki daya za su iya kashewa/Hoto AA

Kanana da matsakaitan masana’antu kalilan ne kawai za su iya tsallake gwajin da ake bukata domin samun masu zuba jari wanda a lokuta da dama.

Hakan na faruwa ne saboda rashin gamsasshen bayanan dokokin shari’a da cikakken bayanin harkokin shiga da fitar kudadensu, da kuma rashin yin amfani da tsarin doka mai kyau.

Wadannan matsalolin suna matukar rage darajar kasuwanci, domin masu son zuba jari ba za su samu gamsuwar cewa kudadensu na hannu nagari ba.

Ba sa samun bayanai

Masu kanana da matsakaita masana’antu a lokuta da dama ba su da masaniyar abubuwan da hukomomin gwamnati ke bukata, kamar zabar ka’idar shari’a da ta fi dacewa da shiga yarjejeniya da masu hannun jari da daraktoci da manyan ma'aikatansu.

Wannan ya kunshi dokokin shari'a na kare kasuwancin kamar yarjejeniya da ma'aikata da kare hakkin mallakar muhimman abubuwansu ciki har da rubuce-rubucensu.

Wannan matsalar ba masu zuba jarin kadai za ta kora ba, har kasuwancin baki daya za ta iya kashewa.

Ba a yi musu abin da ya dace

Yawancin masu kanana da matsakaitan masana’antu na Afirka suna da tunanin cewa lauyoyi masu zaman kansu ba su da dadin hulda, sannan yawancinsu suna tunanin ba sa bukatar aikin lauya sai an kai makura idan ma har za a bukata din.

Suna cewa yana daukar dogon lokaci kafin su samu amsar da suke bukata, sannan dole su yi ta bin bayan aikinsu kafin a musu.

Ba su da tabbacin nawa za su kashe kafin su kai ga karshen lamarin, sannan a lokuta da dama sukan kashe sama da abun da suka yi tsammani.

Hanyar magance matsalar fa?

Masana sun ce ya kamata lauyoyi su samar da hanyoyin saukaka aikinsu ga kananan 'yan kasuwa/Photo AA

Babu shakka kanana da matsakaitan masana'antu na bukatar lauyoyi domin su taimaka musu wajen ‘cika sharuddan kasuwancinsu’ da kuma shirya su wajen habaka harkokinsu.

Akwai bukatar lauyoyi su ilimantar da kananan 'yan kasuwar muhimmancin ayyukansu, wanda hakan na bukatar su mike sosai su yi aiki tukuru.

Ya kamata lauyoyi su kirkiri wani bangare na musamman da zai taimaka wa ’yan kasuwa gyara harkokinsu kafin a samu matsala, a ilimantar da su gibin da ke akwai, sannan a samar musu da yadda za su yi wajen cike gibin.

A karshe, ya kamata lauyoyi su samar da hanyoyin saukaka aikinsu ga kananan 'yan kasuwa ya kuma kasance a fili suke yi.

Hanya mafi sauki da lauyoyin za su yi amfani da ita, ita ce amfani da fasahar zamani wajen kirkirar fasahar da za ta rika amsa bukatun masu neman shawarwarin shari’a ta intanet.

Sannan su bai wa kananan 'yan kasuwa dama su ilimantu da ka'idojin shari'a cikin sauki da rahusa domin su habaka harkokinsu, wanda zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da habaka tattalin arzikin da nahiyar Afirka ke matukar bukata.

Wannan shi ne burinmu a Strand Sahara ta shafinmu na intanet.

Marubuciyar, Rashida Abdulai, lauya ce da ta lashe kyautuka da dama kuma shugabar Strand Sahara, kamfanin lauyoyi na shafin intanet da ke sanya ido kan kasuwanci.

TRT Afrika