Nijeriya ta fuskanci katsewar lantarki a ranar Laraba a yankuna da dama, karo na 12 a shekarar 2024, bayan babban layin dakon lantarkin kasar ya lalace.
Hanyoyin dako da rarraba lantarki na kasar na yawan fuskantar lalacewa, wanda ke janyo karancin lantarki da ke janyo nakasasshen yanayin kasuwanci da hada-hadar tattalin arziki a kasar mafi yawan jama'a a Nijeriya.
Bankin Duniya ya yi kiyasin cewa tattalin arzikin Nijeriya na yin asarar dala biliyan 29 a duk shekara sakamakon rashin samun wutar lantarki da ke haifar da katsewar wutar lantarki a fadin kasar.
Ga dalilan da ke janyo lalacewar hanyoyin rarraba makamashin lantarki a Nijeriya.
Me ka janyo daukewar lantarkin?
Tsaffin kayan samarwa, dako da rarraba wuta na Nijeriya na fuskantar babbar matsala. Hanyoyin dakon lantarkin da tashoshin sauke ta, wadanda wasun su sun fi shekaru 40, na yawan lalacewa.
Kamfanin Dakon Lantarki na Nijeriya mallakin gwamnati ya rawaito raguwar megawat 7.79 a duk megawatt 100 da aka tura ta manyan hanyoyin.
Shekaru da dama da aka dauka ba a zuba jari sun bar hanyoyin isar da lantarkin cikin mawuyacin hali, in ji wani lauya kan makamashi Ayodele Oni mazaunin birnin Legas.
Hare-hare da ta'adin da ake yi kan hanyoyin dakon lantarkin, musamman a arewacin Nijeriya. sun tsananta a shekaru biyun da suka gabata inda TCN ta ce an samu hakan sau 108 kan manyan turakun lantarkinsu.
Gibin samar da lantarki
Wani babban abu kuma shi ne Nijeriya da ke da mutane sama da miliyan 200, na samarwa da rarraba daya bisa uku na abinda za ta iya samarwa na lantarkin wato megawat 13,500.
Kuma duk da kasancewar Nijeriya ta bakwai a duniya da ke da yawan albarkatun iskar gas, Nijeriya na samar da kasa da kashi 10 na lantarkin da Afirka ta Kudu ke samarwa, kasar da yawan ta bai fi daya bisa ukun Nijeriya ba.
Sama da kashi 75 na lantarkin Nijeriya na zuwa ne daga cibiyoyin da ke aiki da iskar gas, wadanda suke kudancin kasar.
Sauran kuma suna samuwa ne daga cibiyoyin samar da lantarki daga ruwa da ke arewa.
Kamfanonin samar da lantarki na aika wa da lantarkin da suka samar zuwa hanyoyin kasa na dakon wutar da gwamnatin tarayya ke kula da su, wadanda suke rarraba su zuwa cibiyoyi 11, sannan a aika wa jama'a.
Ko akwai gyara?
Sama da shekaru goma da suka gabata Nijeriya ta sayar da kamfanin samar da lantarkinta ga 'yan kasuwa, amma duk da haka wutar ba ta inganta ba.
Amma a shekarar da ta gabata gwamnati ta baiwa jihohi 36 damar samar da lantarki tare da dakon ta zuwa ga wuraren amfaninsu.
Jihohi irin su Legas, cibiyar kasuwanci ta kasar, da wasu jihohin biyar sun fara samar da tasu lantarkin.
Kazalika, gwamnatin na aiki da Bankin Duniya don samar da kananan cibiyoyin samar da lantarki daga hasken rana guda 1,000, don fadada samar da wutar a yankunan karkara.
"Ana bukatar kwakkwaran mataki a Nijeriya domin amfana da wuraren samar da lantarki da suke a yankuna daban-daban, misalin makamashi daga hasken rana da za a hade shi da wajen adana shi.
Da kuma manufar cika aikin hanyoyin samarwa da rarraba lantarki na kasa," in ji Sherisse Alexandra, shugaban kasuwanci a kamfanin samar da makamashi mai zaman kansa na 'WATT Rnewable Corporation'.