Rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto da ke arewacin Nijeriya ta ce an kashe mutum hudu tare da sace 18 a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyen Giyawa na karamar hukumar Goronyo ranar Alhamis.
Kakakin rundunar Ahmed Rufai ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar ta Alhamis.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun sace dabbobi da dama da wasu muhimman kayayyaki a kauyen.
Sai dai mazauna kauyen sun ce mutanen da ‘yan bindigar suka sace sun kai talatin.
Labari mai alaka: 'Yan bindiga sun kashe gomman mutane a Sokoto, Zamfara da Binuwai
Ahmed Rufai ya ce bakwai daga cikin mutanen da aka sace sun kubuta inda suka koma gida, ko da yake mutanen kauyen sun tarwatse domin tsira da lafiyarsu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa tuni jami’ansu suka bazama neman ‘yan bindigar kuma yanzu hankula sun kwanta a yankin.
Jihar Sokoto na cikin jihohin da ke fama da kalubale na rashin tsaro sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, wadanda suka sace dubban mutane ciki har da dalibai a shekarun baya bayan nan.
Hukumomi sun sha cewa suna daukar mataki a kan lamarin, inda aka kashe ‘yan bindiga da dama tare da kwace makamansu, amma har yanzu matsalar na ci gaba da faruwa.