Rundunar Sojin Jamhuriyyar Nijar ta ce dakarunta na Operation Harbin Zuma sun kashe ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi 55 a yankin Tafkin Chadi.
Rundunar ce ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter ranar Litinin inda ta ce dakarun sun yi wannan aiki ne tsakanin 6 ga watan Mayu zuwa 28.
Sojojin sun ce a yayin samame daban-daban da aka kai, sun yi amfani da dabarun yaki ta sama da kasa domin kai hari a maboyar 'yan ta'adda da ke kan iyakar kasar da Nijeriya.
Rundunar ta ce daga cikin wadanda ta halaka akwai manyan kwamandojin masu ikirarin jihadi da ake nema irin su Abouzeid da Abou Oumama da Malam Moustapha.
Sojojin sun kuma ce sun lalata motocin na ‘yan ta’adda 13 da babura 13.
Amma sanarwar ta ce akwai sojoji biyu da suka rasa ransu yayin samamen.
Rundunar sojin ta kuma ce wannan nasarar ta sa lagon kungiyoyin ISWAP da ElAO ya karye.
Sa’annan rundunar ta Harbin Zuma ta yi alkawarin kakkabe duk wasu kungiyoyin ‘yan ta'adda da ke addabar al'ummomin garuruwan Bosso da Baga da Goudoumbali da Gashigar.