Burkina Faso na fama da matsalolin rashin tsaro, sakamakon hare-haren 'yan ta'adda da ya somo daga kasar Mali mai makwabtaka. (Ludivine Laniepce / AP)

Hukumomi a Burkina Faso sun ce 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 40 a wani hari da suka kai musu a arewacin kasar.

An kai hari nen kan “tawagar soji da farar hula masu aikin sa-kai ranar Asabar da misalin karfe hudu na yamma", kusa da kauyen Aorema, mai nisa kilomita 15 a arewa maso gabashin birnin Ouahigouya, a cewar wata sanarwa da sakatare janar na lardin Kouilga Albert Zongo ya fitar.

“Mutanen da aka kashe sun hada da masu aikin sa-kai 34 da sojoji shida,” in ji shi.

Ya kara da cewa an jikkata mutum 33 yayin harin.

Kafafen watsa labaran kasar sun rawaito cewa an kashe "gomman 'yan ta'adda” a harin ramuwar gayya da aka kai musu.

Burkina Faso na fama da matsalolin rashin tsaro, sakamakon hare-haren 'yan ta'adda da ya somo daga kasar Mali mai makwabtaka.

A makon jiya, an kashe akalla farar-hula 44 a hare-hare biyu da 'yan ta'adda suka kai arewacin Burkina Faso.

TRT Afrika da abokan hulda