Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Mauritaniya inda ake sa ran ‘yan ƙasar za su yanke hukunci kan ko su sake zaɓar shugaban mai ci Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani a matsayin sabon shugaban ƙasar.
Kusan mutum miliyan 1.9 ne suka yi rajistar zaɓe inda ake sa ran za su zaɓi tsakanin mutum bakwai waɗanda suke takarar shugaban ƙasar.
Ghazouani ya hau kan karagar mulki ne bayan zaben shekarar 2019 wanda ya zama karo na farko da aka miƙa mulki tsakanin zaɓaɓɓun shugabannin ƙasa biyu tun bayan da ƙasar ta samu ‘yancin kai daga Faransa a 1960, inda bayan haka aka yi ta fama da juyin mulki tun daga 1978 zuwa 2008.
Za a buɗe rumfunan zaɓe da misalin ƙarfe 7:00 na safe agogon ƙasar sannan a rufe 07:00 na dare duk a ranar Asabar.
Ana sa ran sakamakon farko-farko na zaɓen ya soma fitowa a ranar Asabar da dare. Sai dai sanar da gaba ɗaya sakamakon zaɓen ana sa ran yin shi ne a ranar Lahadi ko kuma Litinin.
Ghazouani wanda tsohon janar ne na soja kuma shugaban ƙasar mai ci a yanzu, shi ne wanda ake ganin zai samun wa'adi na biyu, inda masu lura da al'amuran yau da kullum ke duba yiwuwar samun nasara a zagayen farko idan aka yi la'akari da rarrabuwar kawuna na 'yan adawa da kuma irin kuɗin da jam’iyyar shugaban ƙasa ke da shi.
Idan ba a samu wanda ya samu nasara a zaɓen ba, za a je zagaye na biyu a ranar 14 ga watan Yuli.
Yayin da yankin Sahel a shekarun baya-bayan nan ya fuskanci jerin juyin mulkin soji da kuma hare-hare daga kungiyoyi masu dauke da makamai, za a iya cewa ba laifi ƙasar Mauritaniya na da kwanciyar hankali.
Bayan barkewar cutar korona da kuma yakin Ukraine, Ghazouani ya sanya yaki da talauci da tallafa wa matasa a matsayin abubuwan da ya sa gaba.
Sama da kashi 70 cikin 100 na al'ummar Mauritania ba su kai shekaru 35 ba, inda matasa ke daɗa sha'awar fatan samun kyakkyawar makoma a Turai ko Amurka.
An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki matuƙa daga kashi 9.5 wanda ya kai a 2022 zuwa kashi 5 a 2023, inda ake sa ran a ƙara samun raguwa zuwa kashi 2.4 a 2024.