Aƙalla mutum 26 ne suka mutu suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a cikin garin Kano. Hoto: FRSC File Photo 

Aƙalla mutum 26 ne suka mutu suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a cikin garin Kano, inda wasu mutum 53 suka jikkata.

Hukumar Kula da Kare Afkuwar Hadurra ta Nijeriya FRSC wadda ta tabbatar da labarin ta bakin shugabanta reshen jihar Kano Ibrahim Abdullahi, ya ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3.15 na tsakar daren Litinin.

Kazalika dabbobi guda 10 sun mutu, waɗanda duk ake tafiya da su a cikin motar.

“Hatsarin ya faru ne a kan gadar Na’ibawa a lokacin da motar ta ƙwace wa direban saboda bacci da yake fsigarsa har motar ta jirkice ta faɗi,” in ji wani fasinja da ke cikin motar a kusa da direban a lokacin da abin ya faru.

Sai dai kwamandan na FRSC ya ce lamarin ya faru ne sakamakon tsananin gudu da kuma lodi da ya yi wa motar yawa har ya jawo faɗuwar motar. Ya ce likitoci sun tabbatar da mutuwar mutum 25.

“Da samun labarin hadarin ne sai muka tura tawagar agajin gaggawa don ceton mutane,” in ji Ibrahim Abdullahi.

Fasinjan nan ya ce motar ta taso ne daga Mai’aduwa a jihar Katsina zuwa birnin birnin Ibadan na jihar Oyo a kudu maso yammacin ƙasar.

Kwamandan FRSC ya ƙara da cewa a yayin aikin ceton an gano babura shida da wayoyin hannu 10 da dabbobi kamar awaki da raguna da masara da kuma naira 4,000.

Abdullahi ya ce an miƙa duka kayayyakin ga rundunar ‘yan sanda.

TRT Afrika