Mutum aƙalla takwas sun mutu bayan wata 'yar ƙunar-baƙin-wake ta tashi bam da ke jikinta a ƙaramar hukumar Gwoza ta Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya ranar Asabar.
Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno ASP Nahum Kenneth Daso ya fitar ce ta tabbatar da mutuwar mutanen. Ta ƙara da cewa mutum kimanin 15 ne suka jikkata.
Harin ya yi sanadin "mutuwar matar da jaririnta da mutum shida, sannan mutum goma sha biyar da suka jikkata yanzu haka suna Babban Asibitin Gwoza inda suke jinya", in ji Kenneth.
Tun da farko kamfanin dillancin labaran News Agency of Nigeria (NAN) ya ambato Kwamishinan 'yan sandan Jihar Borno Yusuf Lawal yana cewa mutum shida ne suka mutu.
Ganau sun ce matar, wadda ke goye da jariri, ta tashi bam ɗin ne a wani wurin biki a Marrarraban Gwoza.
NAN ya ambato wani ganau mai suna Muhammed Kasim yana cewa "mun ji babbar ƙarar fashewar wani abu da kuma tashin ƙura; sannan muka ga gangar jikin mutane a ƙasar.”
Ya ce an garzaya da mutanen da suka jikkata asibitin da ke Gwoza domin yi musu magani.
'Kisa a maƙabarta'
Kazalika bayanai sun nuna cewa wani ɗan ƙunar-baƙin-waken ya tayar da bam a maƙabarta lokacin da aka je binne mutanen da suka rasu a harin bam na farko.
Mutumin, wanda ya saje a cikin masu jana'iza, ya kashe mutum ɗaya tare da jikkata wasu.
Amma shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno Barkindo Saidu ya shaida wa wasu kafofin watsa labarai cewa mutum 18 ne suka mutu sannan kusan 30 suka jikkata a hare-haren na ƙunar-baƙin-wake.
Tuni dai rundunar sojojin Nijeriya da ke aiki a yankin ta sanya dokar hana fita a Gwoza.
Jihar Borno ta kwashe shekaru da dama tana fama da hare-haren 'yan Boko Haram waɗanda suka yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.
Hukumomi a ƙasar sun ce sun murƙushe mayaƙan Boko Haram, ko da yake akan fuskanci hare-haren gyauronsu lokaci zuwa lokaci.