Mali ta dade tana fama da rikicin masu ikirarin kishin Musulunci kuma jagororin juyin mulki./Hoto: Reuters

Dakarun Mali da sojojin haya na Wagner da Rasha ke mara wa baya suna amfani da cin zarafin mata da "take hakkin dan Adam" wajen yada ta'addanci, a cewar wani rahoto na jami'an da ke sanya ido kan takunkumai na Majalisar Dinkin Duniya (MDD).

Kazalika masu sanya idon sun gargadi Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa "ana kitsa laifukan cin zarafi da dakarun Mali da na kasashen ketare ke aikatawa ne.

Sun ce "dakarun kasashen wajen su ne mambobin kungiyar sojojin haya ta Wagner."

Mali ta dade tana fama da rikicin masu ikirarin kishin Musulunci kuma jagororin juyin mulki da suka hambarar da gwamnatin kasar a shekarar 2020 da kuma 2021, sun hada kai da sojin haya na Wagner a shekarar 2021.

Akwai kimanin sojojin haya na Wagner 1,000 a Mali. Kasashen yankin Yammacin Afirka sun sha nuna damuwarsu kan aikace-aikacen sojojin Wagner a kasar Mali.

Amurka ta sanya takunkumai a kan Wagner da jami'ai a Mali kuma ta yi gargadi kan abin da ta kira dagula al'amura da sojojin kugiyar ke yi.

"Mun yi amannar cewa ana cin zarafin mata da sauran manyan laifukan take hakkin dan Adam da dokokin kasa da kasa musamman a bangaren sojojin hayan don ci gaba da aikata ta'addanci," kamar yadda masu sanya ido kan takunkumai na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) suka bayyana.

Sai dai kungiyar sojojin haya ta Wagner ba ta ce komai ba kan batun. Jagoran kungiyar Yevgeny Prigozhin ya jagoranci wani bore a kan sojojin Rasha a karshen watan Yuni.

Bangaren Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin a watan Mayu ya zargi dakarun Mali da kuma "fararen sojoji masu dauke da makamai" da kisan mutum 500 da azabtarwa da cin zarafin wasu da dama lokacin wani aikin kwana biyar a tsakiyar Mali a bara.

Rasha ta ce aikin "ya taimaka wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali".

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'a a ranar 30 ga watan Yuni don a kawo karshen aikin samar da zaman lafiya da aka kwashe shekara 10 ana yi a Mali, bayan jagoran juyin mulkin kasar ya ba dakarun majalisar su 13,000 umarnin su fice daga kasar — abin da Amurka ta ce kungiyar Wagner ce ta kitsa shi.

Reuters