Ranar Asabar Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da rikicin kabilanci da kuma kashe 'yan kabilar Masalit a birnin El Geneina na Yammacin Darfur.  / Hoto: AP

Dakarun sa-kai na Rapid Support Forces, RSF, sun ce sun kwace babban sansanin 'yan sanda da ke Khartoum a yayin da suke ci gaba da fafatawa da sojojin Sudan.

Wata sanarwa da RSF ta fitar ranar Lahadi ta ce ta karbe daukacin ikon tafiyar da sansanin zaratan 'yan sanda na Central Reserve Police da ke kudancin Khartoum kuma ta wallafa wani bidiyo da ke nuna mayakanta suna murna a cikinsa, wasu daga cikinsu suna fito da akwatunan da aka ajiye alburusai.

Daga bisani rundunar ta ce ta kwace motocin a-kori-kura guda 160, motocin harba makamai 75 da kuma tankokin yaki 27. Kamfanin dillacin labarai na Reuters bai tantance sahihancin bidiyon ba. Kazalika sojoji da 'yan sanda ba su ce uffan ba kan ikirarin da RSF ta yi.

Tun ranar Asabar da la'asar yaki ya yi kamari a birane uku da suka hada babban birnin kasar - Khartoum, Bahri da Omdurman - a yayin da rikici tsakanin sojin Sudan da dakaru RSF ya shiga mako na 11.

"Tun da safiya muke jin ana barin wuta da harba makaman atilari da makaman harbo jiragen sama na RSF a arewacin Omdurman," a cewar Mohamed al Samani, mai shekara 47, a hira ta wayar tarho da Reuters.

Ganau sun bayar da rahoton karuwar rikici a kwanakin nan a Nyala, birni mafi girma da ke lardin yammacin Darfur.

Ranar Asabar Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da rikicin kabilanci da kuma kashe 'yan kabilar Masalit a birnin El Geneina na Yammacin Darfur.

Yakin ya fi shafar Khartoum da El Geneina, ko da yake a makon jiya rikicin ya yi kamari a yankunan Darfur da Kordofan da ke kudancin kasar.

Rikicin na baya-bayan nan ya yi sanadin mutuwar gomman fararen-hula a Darfur, a cewar wani likita.

Da yake magana daga jihar Kudancin Darfur, likitan ya ce "an kashe fararen-hula 12 a Nyala".

Yakin ya yi kamari ne bayan bangarorin biyu sun gaza yin biyayya ga jerin yarjejeniyoyin tsagaita wuta da Amurka da Saudiyya suka shiga tsakani don kullawa. A makon jiya ana dage zaman tattaunawar da ake yi a birnin Jeddah.

Rundunar sojin Sudan ta aika zaratan 'yan sanda na Central Reserve Police domin fafatawa ta kasa da dakarun RSF a makonnin baya bayan nan. A baya ana amfani da su ne domin ayyuka na musamman da suka hada da kwantar da tarzomar da aka yi ta kyamar juyin mulkin 2021.

An kashe kusan mutum 2,800 a Sudan tun da rikici ya barke a Khartoum ranar 15 ga watan Afrilu, a cewar sabbin alkaluma daga cibiyar ttara bayanai kan rikicin ta Armed Conflict Location and Event Data Project.

Hukumar kula da masu kaura ta duniya ta ce akalla mutum miliyan biyu aka raba da muhallansu a cikin kasar sannan kusan mutum 600,000 sun tsere daga Sudan zuwa wasu kasashen tun bayan soma yakin.

Reuters