Zulum ya dakatar da ayyukan 'yan jari-bola cikin gaggawa a kananan hukumomi 27 da ke fadin jihar Borno. /Hoto: Shafin Facebook/Gwamnatin jihar Borno

Gwamnan Borno da ke arewacin Nijeriya Babagana Umara Zulum ya ba da umarnin dakatar da ayyukan ‘yan jari-bola a jihar, a yayin wata ziyara da ya kai yankin Bulumkutu da ke jihar ranar Litinin.

Gwamnan ya ci karo da wasu tarin karafa na gwamnati da ake zargi masu sana'ar jari bola ne suka lalata su.

Dakatarwar ta shafi kananan hukumomi 27 da ke fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa a shekarun baya, masu irin wannan sana'a da dama sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren mayakan Boko-Haram saboda suna zuwa yankunan da babu mutane sosai don barnata kayayyaki.

Kazalika Zulum ya ce ana zargin wasu daga cikin 'yan jari-bola da sace dukiyoyin gwamnati da jama'a.

“Yawancin wadannan kayayyaki na gwamnati ne, ga su nan muna gani, akwai fitulun kan titi, da fal-wayoyin wutar lantarki da tankoki mallakin kamfanonin sadarwa da dai sauransu.

“Irin wadannan sace-sace na iya kawo cikas ga ayyukan gwamnatocin jihohi da na tarayya," a cewar Gwamna Zulum.

“Ba za mu bari a ci gaba da aikata irin wannan aika-aika ba, na kuma yi Allah wadai da kaukasar murya tare da ayyana dokar hana ayyukan jari-bola a jihar Borno har sai an samu sanarwa a nan gaba.

''Zan rattaba hannu kan wata doka da za ta hana duk wani nau’in ayyukan 'yan jari-bola a Borno,” in ji Zulum.

Gwamnan ya ce an bayar da wannan umarnin ne domin a tsabtace harkokin kasuwanci da kuma kare rayukan su kansu masu sana’ar jari-bola a fadin jihar baki daya.

Ya yi gargadin kan cewa gwamnatin Borno za ta hada gwiwa da jami’an tsaro don aiwatar da dokar yadda ya kamata ta hanyar zartar da hukunci mai tsauri kan wadanda suka karya ta.

TRT Afrika