Shugaban kamfanin BUA a Nijeriya, Abdulsamad Rabiu, ya yaba da sabon matakin da babban bankin kasar ya dauka na karya darajar naira domin daidaita farashinta a kasuwar duniya.
Gwamnatin Nijeriya ta dauki matakin mayar da dalar 630 daga 465 domin daidaita farashinta da na bayan fage wanda yake sama da 700.
A wata hira da Abdulsamad ya yi da kafar watsa labarai ta CNBC, ya bayyana cewa yana kyautata zaton za su samu tagomashi matuka sakamakon wannan matakin.
A cewarsa, a duk wata kamfaninsa yakan samu gibin dala miliyan 50 zuwa 60 wanda a cewarsa ba za su iya samun kudin daga babban bankin Nijeriya a farashin gwamnati ba sai dai su nema a farashin bayan fage.
“Abin da wannan tsarin yake nufi a ganina shi ne zai ba masu zuba jari damar kawo kudi. Saboda farashin gwamnati a kullum yana kasa da asalin yadda farashin yake. Hakan ya sa masu zuba jari da dama ba su sakin jiki su kawo kudi a farashin da duka muka san ba shi ne asalin farashi ba,” in ji Abdulsamad.
Ya bayyana cewa yana tunanin da wannan sabon tsarin, za a samu daidaito kuma za a samu masu zuba jari da za su shiga kasar su zuba jari.
Wadannan kalaman na shugaban kamfanin na BUA na zuwa ne a daidai lokacin da ake ruwaito cewa kamfaninsa da sauran manyan kamfanoni masu zaman kansu na Nijeriya sun tafka babbar asara sakamakon karya darajar naira da babban bankin kasar ya yi.