Shugabar Tanzania ta kai ziyarar kwanaki uku Malawi a farkon watan Yuli. Hoto/ Malawi Presidency

Kasashen Malawi da Tanzania sun sanar da shirinsu na cire takunkumin da ke tsakaninsu inda a halin yanzu za a ci gaba da zirga-zirga da kuma kasuwanci tsakanin kasashen biyu ba tare da shinge ba.

Cire wannan shingen zai ba kasashen biyu damar amfana tsakaninsu, kamar yadda Shugabar Tanzania Samia Suluhu ta bayyana.

Suluhu ta je Malawi domin ziyarar kwanaki uku inda ta zama bakuwa ta musamman a taron cikar kasar Malawin shekara 59 da samun ‘yancin kai a ranar 6 ga watan Yuli.

Darakatar watsa labarai ta fadar gwamnatin Tanzania ta fitar da sanarwa inda ta ce Shugaba Suluhu “ta jaddada bukatar cire shingen da ke kan iyaka tsakanin Tanzania da Malawi domin habaka kasuwanci.”

“Shugaba Suluhu da takwaranta na Malawi, Lazarus Chakwera sun bukaci ministocin da lamarin ya shafa daga duka kasashen da su zauna su amince kan yadda za a cire takunkumin kan iyaka domin cimma bukatun duka gwamnatocin,” in ji sanarwar.

Karancin kasuwanci

A bangarensa, Shugaba Chakwera ya koka kan karancin kasuwancin da ke tsakanin Malawi da Tanzania, inda ya ce akasarin kayayyakin da ya kamata a kai tsakanin kasashen biyu ana rasa su ta hanyar “fasa kwabri”.

“Hakan na sa kasashen biyu na asarar kudin shiga,” kamar yadda Chakwera ya bayyana a ranar Juma’a a lokacin wani taron manema labarai a Lilongwe babban birnin Malawi.

Ya kara da cewa tsarin da aka yi na cire shingen da ke tsakanin iyakokin kasashen biyu zai hana fasa kwabri.

“Malawi da Tanzania sun shirya amfani da makwaftakarsu domin bunkasa hadin kai tsakaninsu da kuma amfani da hanyar da ke tsakaninsu wurin bunkasa kasuwanci,” in ji shi.

Alkaluman kasuwanci

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa Tanzania na fitar da kayayyaki zuwa Malawi da suka kai na dala miliyan 60.74 a 2022, inda akasarin kayayyakin na gyara ne ko tsafta da suka hada da zannuwan gado da sabulai.

Malawi kuwa a dayen bangaren ta fitar da kayayyaki ga Tanzania da suka kai na kimanin dala miliyan 20, inda kayayyakin da ke kan gaba sun hada da waken soya da garin waken soya da plankin katako.

Haka kuma Suluhu ta yi maraba da matakin Malawi na soma koyar da harshen Swahili a makarantun kasar inda ta ce “harshen zai kara hada kan kasashen biyu.”

Malawi da Tanzania sun kuma kara saka hannu kan wata yarjejeniya ta hadin kai kan batun kimiyya.

TRT Afrika