Ba wannan ne karo na farko da aka sauya sansanin masu yi wa kasa hidima a Nijeriya ba saboda rashin tsaro. Hoto/NYSC

Hukumar da ke kula da masu yi wa kasa hidima ta Nijeriya NYSC ta sanar da sauya sansaninta na Jihar Filato daga Mangu zuwa Doi-Du da ke jihar.

Hukumar bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar a shafinta na sada zumunta tana mai cewa a halin yanzu za ta yi amfani da sansanin wucin-gadi na Waye Foundation da ke Doi-Du don horar da masu yi wa kasa hidima.

Duk da NYSC ba ta sanar da dalilinta na sauya sansanin masu yi wa kasa hidima ba, amma wasu na ganin hakan na da nasaba da rikicin da ake yi a yankin da kuma matakan da gwamnati ke dauka don dakile shi.

A makon da muke ciki Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang ya saka dokar hana fita ta awa 24 a Karamar Hukumar Mangu sakamakon hare-hare.

Ana yawan samun rikici a al’ummomin da ke karamar hukumar wadanda akasari suke da alaka da kabilanci.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa an kai sabbin hare-hare a yankin ranar Asabar da dare inda aka kashe akalla mutum tara.

Haka kuma kamfanin dillancin labaran ya ce Babban Kwamandan Soji na Rundunar Operation Hadin Kai da ke aiki a Jihar Filato ya mayar da shalkwatar rundunar zuwa Mangu domin dakile rikicin da ake yi.

Ya kuma bayyana cewa sojojin za su rinka aiki a yankin har sai an samu zaman lafiya.

Ba wannan ne karo na farko da aka sauya sansanin masu yi wa kasa hidima a Nijeriya ba saboda rashin tsaro.

A 2014 hukumar ta NYSC ta taba dauke sansanoninta na yi wa kasa hidima daga Jihohin Borno da Kano da Bauchi da Adamawa da Gombe da Jigawa da Yobe saboda rashin tsaro.

Haka kuma a bara rashin tsaron ya sa aka sauya sansanin masu yi wa kasa hidima da ke Tsafe ya koma Gusau a Jihar Zamfara.

TRT Afrika