Wasu sojojin gwamnati uku a kan babur a yayin da suke dawo wa daga fagen daga a Kibati. arewa da garin Goma na gabashin Jumhuriyar Dimokradiyyar Kongo. / Hoto: AP

Wasu da ake zargin 'yan tawayen ADF da ke da alaka da kungiyar ta'adda ta Daesh sun kashe fararen hula 20 a lardin Ituri na arewa maso-gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, inji majiyoyin yankin.

"A ranar Talata aka kama mutanen a yayin harin da ADF suka kai" a Babila babombi, wani yanki da ke Mambasa, yankin da ke yawan fuskantar hare-hare daga ADF da sauran kungiyoyin tayar da kayar baya, in ji jami'in 'yan sanda Matadi Muyapandi a ranar Alhamis.

Ya ce "An kashe mutane 20 - maza 16 da mata hudu," inda ya kara da cewar wasu mutum hudu da suka gudu sun jikkata kuma ana kula da lafiyarsu a asibiti.

"An yanke kawunan mutanen, yadda dai kungiyar ta saba" yi wa mutanen da take kama wa, asalin ADF 'yan tawayen Uganda ne, wadanda a cikin shekaru ukun da suka shude suka yadu a gabashin DRC, suna kashe dubunnan fararen hula.

An samu yawaitar kai hare-hare a 'yan watannin nan.

An kama fararen hular a kauyuka da dama da aka kai wa hare-hare, sannan aka tara su waje guda a daji tare da kashe su, in ji Rams Malikidogo, wani mai kare hakkokin dan adam a Mambasa da ke Jumhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

"Wadanda aka kashe din masu hakar ma'adanai, 'yan kasuwa da manoma ne," in ji wani ma'aikacin agaji na yankin da aka tuntuba ta wayar tarho amma ya nemi a boye sunansa.

Ya kara da cewa an aikata kisan ne a wani waje kebantacce. "Muna bukatar zuwa sojoji don su nemo gawarwakin tare da binne su cikin daraja."

A shekarar 2019 ADF suka yi mubaya'a ga kungiyar ta'adda ta Daesh, wadda ta ke nuna wa a matsayin reshenta na Tsakiyar Afirka. Ana zargin ADF da kashe fararen hular Kongo, tare da kai hare-hare a makociyar kasar Uganda.

Tun karshen 2021, sojojin Kongo da na Uganda na kai farmakan hadin gwiwa kan ADF a Arewacin Kivu da lardin Ituri, amma har yanzu ba su iya hana kai hare-hare kan fararen hula ba.

Sai dai kuma wasu kwararru sun yi amanna cewa farmakan sun janyo 'yan ta'addar guduwa zuwa yankunan da ke da wahalar zuwa, inda suke ci gaba da kashe fararen hula.

TRT World