Hukumomin Uganda sun ce mayakan ADF ne suka kai harin sai dai mayakan na ADF ba su ce komai ba. Hoto/ Reuters Archive

Akalla mutum 25 suka rasu sakamakon wani “harin ta’addanci” da aka kai wata makaranta da ke yammacin Uganda ta kan iyaka da Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo.

Mai magana da yawun ‘yan sandan kasar ya bayyana cewa kungiyar Daesh da ke da alaka da Allied Democratic Forces ADF ce ta kai wannan harin.

“Zuwa yanzu gawarwaki 25 aka gano daga makarantar kuma tuni aka kai su asbitin Bwera,” in ji mai magana da yawun ‘yan sandan Fred Enanga.

Mista Enanga ya bayyana cewa ADF, wadda ke kai hare-hare a gabashin Dimokradiyyar Kongo ta kai hari a wata makarantar sakandire kusa da Bwera “inda aka kona dakin kwanan dalibai aka kuma sace kayayyaki”.

“An samu an ceto wasu mutum takwas wadanda yanzu haka suke cikin wani hali a asibitin Bwera,” in ji shi a sanarwar da ya fitar. ADF ba ta ce komai ba dangane da wannan harin.

Haka kuma ‘yan sandan ba su yi karin haske ba kan mutum nawa ne dalibai cikin wadanda suka mutu.

Tuni sojoji da ‘yan sanda suka bazama neman maharan wadanda suka fantsama a cikin dajin Virunga, wanda ke kan iyaka da Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo inda nan ne matattarar ADF.

Tun da farko kungiyar ADF ta sha kai hare-hare gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo tun a shekarun 1990 inda aka zarge su da kashe dubban farar hula.

Tun daga 2019, wasu daga cikin hare-haren ADF a DRC kungiyar Daesh ko kuma IS ce ke daukar nauyin kai su.

AFP