Rikicin Sudan ya soma ne tun a watan Afrilu kuma babu alamun zai kawo karshe a halin yanzu. Hoto/Reuters

Daga Sylvia Chebet

Musayar wuta ba kakkautawa, gidaje na kamawa da wuta, da kuma baraguzan da suka bazu bayan harbo jirgin saman yakin soji duk sun girgiza birnin Omdurman da ke arewa maso yammacin Khartoum babban birnin Sudan, a daidai lokacin da ake sabuwar arangama tsakanin sojojin kasar da abokan gabarsu.

Haka kuma yarjejeniyar tsagaita wuta a lokacin Babbar Sallah wadda aka yi niyyar ta kawo sauki ga jama’a ta kare da zama wani sabon rikici.

A ranar 4 ga watan Yuli kadai, asibiti daya ya karbi sama da farar-hula100 da suka samu raunuka a daidai lokacin da sojojin Sudan da dakarun RSF suka yi musayar wuta a Omdurman, kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan yakin Sudan ta bayyana.

Asibitin Al-Nou, mai nisan kilomita kadan daga fagen yaki ta arewacin kasar, ya bayar da rahoton samun karin wadanda suka samu rauni sakamakon rikicin a wasu wurare da ke makwaftaka.

An raunata da kuma kashe dubban mutane tun bayan da aka soma rikicin. Hoto/Reuters

Domin taimaka wa asibitin Al Nou, sai kungiyar agaji ta Volunteer Initiative ta wallafa bukatar gaggawa a shafin Facebook inda ta bayyana cewa lamarin da ake ciki a asibitin yanayi ne na “bala’i”.

“Tun safe, asibitin Al Nou yana fama da karancin ma’aikata da magungunan asibiti sakamakon arangamar da ake yi tun da asuba, kuma da rauni mai tsanani, lamarin ya kara kamari,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Kwamitin wucin gadi na kungiyar likitocin Sudan ya bukaci jami’an lafiya da su je asibitin Al Nou domin kai taimako, inda suka ce suna matukar bukatar likitocin da ke aikin tiyata tare da kayayyakin da ake bukata wurin tiyatar da allurar bacci.

Musayar wuta

A daidai lokacin yaki ya soma addabar wasu sassa na birnin Khartoum, inda ya zo daidai da lokacin da bukukuwan Sallah ke kawo karshe, tunanin yarjejeniyar tsagaita wuta za ta kawo sauki sai ya zama rikicin ya fi muni.

Rikici ya kara kamari tun bayan da aka kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta ta bayan Babbar Sallah. Hoto/Reuters

Rikicin da aka yi a Omdurman tsakanin 2 zuwa 4 ga watan Yuli ya fi zafafa fiye da makonnin da suka gabata.

Wasu daga cikin masu sa ido sun ce shi ne rikici mafi muni tun bayan da aka soma rikicin.

Kungiyar da ke sa ido kan yakin Sudan ta bayar da rahoton cewa hare-haren bam ya fada kan gidaje a layin Al-Radamia a ranar 3 ga watan Yuli, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku da kuma raunata biyar.

“A daidai wannan lokaci, abin da muke ji kawai shi ne karar harsasai. Ban san abin da ke faruwa ba,” in ji Abulgassim Ibrahim Hassan, wani mazaunin Al-Taif da ke Khartoum a tattaunawarsa da TRT Afrika.

A Lahadin da ta gabata, wani mazaunin na Khartoum ya bayyana cewa tsananin yakin da ake yi ne ya tashe shi daga bacci. Wani kuma ya ce karar jiragen yaki ne suka tashe shi daga bacci.

Saba yarjejeniyar tsagaita wuta

Ana yawan sanar da yarjejeniayr tsagaita wuta a matsayin daya daga cikin hanyoyin sulhu, inda hakan ke nuna alamun yunkuri daga bangarorin da ke rikici da juna na kokarin kawo karshen rikicin da suke yi da makamai.

Kwararru kan zaman lafiya da sasancin rikici sun bayyana yarjejeniyar tsagaita wuta a matsayin abin da ake sabawa dagangan sakamakon wasu dalilai da suka hada da harzukawa.

Musulmai sun yi amfani da lokacin yarjejeniyar tsagaita wuta domin halartar Sallar Idi. Hoto/Reuters

A wasu lokuta, bangarorin da ke rikici da juna na ayyana yarjejeniyar tsagaita wuta saboda wasu dalilai, domin sake samun makamai da sararawa har ma da kara daukar dakaru musamman idan suka ga dakarunsu na raguwa ko kuma karsashinsu ya ragu.

Sai dai ba su bayyana haka,” kamar yadda Dakta Mustafa Yusuf Ali, shugaban Cibiyar Nazarin Rikici ta Kusurwar Afirka ya bayyana, a hirarsa da TRT Afrika.

A lokuta da dama, bangarorin waje kan sa masu rikicin su tsahirta saboda ayyukan jinkai da kuma taimaka wa farar hula wadanda ke cikin wahala.

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta baya-bayan nan kungiyar RSF ce ta soma kira da a yi ta, sa’annan bayan kwana daya Rundunar Sojin Sudan ta nema, inda duka suka kira yarjejeniyar da ta “gaba-gadi”.

“Sun ce sun tsagaita wuta ne saboda Babbar Sallah, inda suka numfasa suka kara dawowa da karfinsu, wanda hakan ya lalata jigon yarjejeniyar,” in ji Ali.

Sama da mutum miliyan biyu suka rasa muhallansu sakamakon wannan rikicin. Hoto/Reuters

Kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yan ci rani ta Duniya ta bayyana, akwai karin mutum miliyan 2.2 da suka rasa matsuguninsu a cikin kasar inda mutum 645,000 suka gudu daga kasar.

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta lokacin Babbar Sallah ita ce ta bakwai tun bayan da aka soma yakin.

A baya, Amurka da Saudiyya da kuma Kungiyar Tarayyar Afirka duk sun yi kokarin sasanci amma lamarin ya gagara.

A baya Shugaban Sojin Sudan Al Burhan da kuma Daglo na RSF abokai ne. Hoto/Reuters

Yunkuri da ake yi na neman yarjejeniyar tsagaita wuta shi ne samar da damar tattaunawa wadda idan aka samu nasara za ta iya biyo baya da yarjejeniyar zaman lafiya.

Sai dai lamarin ya kara kamari a rikicin da ake yi na neman iko da mulkin kasar tsakanin sojojin sudan da kuma rundunar RSF.

Kowane bangare na son ganin bayan abokin gabarsa. Kuma a duk ranar rikicin yana kara kazancewa fiye da baya, sa’annan yiwuwar samun zaman lafiya na dada raguwa.

TRT Afrika