Iyalai dama sun tsere wa hare-haren dakarun RSF a jihar  El Gezira ta Sudan / Hoto: Reuters  

Fiye da mutum miliyan ɗaya ne suka tsere wa yakin Sudan sannan suka isa makwabciyar ƙasar Sudan ta Kudu, lamarin da ke nuna mummunan bala'in rikicin jin ƙai da yakin na kusan shekara biyu ya haifar, a cewar hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata.

Wasu sabbin bayanai daga hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) sun bayyana cewa, mafi yawan 'yan gudun hijirar 'yan asalin Sudan ta Kudu ne waɗanda a baya suka nemi mafaka a Sudan a lokacin yakin basasar da ƙasar ta fada ciki.

Dubban 'yan kasar Sudan waɗanda suka rasa matsugunansu a karon farko sakamakon yakin da ake fama da shi tare da wasu 'yan kasashe daban da ke zaune a Sudan ne suka nemi mafaka a Sudan ta Kudu.

"Tun bayan barkewar yakin a watan Afrilun 2023, fiye da mutum 770,200 ne suka tsallaka ta hanyar Wunthou (Joda) da ke kan iyakar Sudan da Sudan ta Kudu," a cewar hukumomi.

Manyan hanyoyin tsallakawa

Wasu ƙarin dubban mutane sun tsallaka zuwa Sudan ta Kudu ta manyan iyakokin ƙasar, ciki har da Majokyinthiou da ke Arewancin jihar Bahr el Ghazal da Panakuach a jihar Unity da kuma Abyei Amiet a yankin gundumar na Abyei.

Hukumar IOM da UNHCR na ƙara nuna fargaba game da yawan 'yan gudun hijirar da ba a taba ganin adadinsu ba, suna masu nuna matukar damuwarsu game da yadda rikicin ke kara ta'azzara.

Hukumomin biyu na kan ba da tallafin ƙudade da na sufuri da matsugunai da kuma sauran kayayyakin da ba na abinci ba, tare da samar da tsaftataccen ruwa da kuma taimakon kula da lafiyar kwakwalwa da dai sauransu.

"Shigar mutane fiye da miliyan ɗaya zuwa Sudan ta Kudu wani yanayi mai ban tsaro da tashin hankali ne, wanda ke nuna girman matsalar da ake ciki,'' a cewar Sanaa Abdalla Omer, mataimakiyar wakilin hukumar UNHCR a Sudan ta Kudu.

'Taimakon ceton rai'

''A kowace rana, ana tilasta wa wasu ƙarin iyalai ɗaukar mataki na tsere wa rikicin Sudan tare da neman mafaka.

UNHCR na aiki tare da gwamnati da sauran abokan hulda don isar da tallafin ceton rai da suka hada da kayayyakin bukatu na yau da kullun ga iyalan da suka rasa matsugunansu da kuma al'ummomin da suka ƙarbi baƙuncinsu," in ji Sanaa Omer.

Omer ya kuma yaba wa al'ummar Sudan ta Kudu bisa ga karamcin da suka nuna wajen ƙarbar masu neman agaji, sai dai ya jaddada cewa ba za su iya su kadai ba.

Sanaaa ta yi kira ga kasashen duniya da su kara ƙaimi wajen tallafawa saboda iyalan da suka rasa matsugunansu da kuma al'ummomin da suka karbi bakuncinsu sun samu kayayyakin da suke buƙata cikin gaggawa.

"Yayin da ake ci gaba da yaki a Sudan, hukumar IOM ta himmatu wajen magance buƙatun gaggawa na waɗanda aka tilasta wa yin hijira zuwa Sudan ta Kudu, sannan a shirye take ta matsa kaimi wajen tabbatar da hakan,'' a cewar Vijaya Souri, shugabar tawagar IOM a Sudan.

AA