Adadin waɗanda zazzaɓin Lassa ya kashe a Nijeriya tun daga farkon shekarar nan ya kai 22, in ji hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasar, NCDC.
Wata sanarwar da hukumar ta fitar ranar Laraba ta ce zazzaɓin ya yaɗu zuwa jihohi bakwai a ƙasar inda aka yi wa mutum 484 da ake tsammanin sun kamu da cutar gwaji kuma aka tabbatar da cewa 143 daga cikinsu sun kamu da cutar.
Hukumomi dai sun amince da magunguna iri uku domin daƙile tasirin cutar.
A bara dai cutar ta kashe aƙalla mutum 90.
Zazzaɓin Lassa, cuta ce da ke yaɗuwa daga dabbobi zuwa mutane wadda aka fi samu a ƙasashen Afirka ta Yamma, kuma an fara gano ta ne a shekarar 1969 jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
A watan Janairun 2019, gwamnatin Nijeriya ta ayyana dokar ta-ɓaci sakamakon zazzaɓin Lassa.
Cutar wadda ke yaɗuwa ta hanyar kashin ɓera za ta iya yaɗu daga mutum zuwa wani mutum kuma tana janyo zazzaɓi mai iya kisa.
Hukumomi suna kira ga mutane su kiyaye haɗuwa da ɓera da ire-irensu