Ƙungiyar Sahel Alliance ta ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar na shirin kafa wata rundunar soji ta haɗin gwiwa mai dakaru 5,000.
Ministan Tsaron Nijar Janar Salifou Modi ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Nijar RTN a ranar Talata.
Ministan ya bayyana cewa sabuwar rundunar wadda ta ƙunshi sojojin ƙasa da na sama da kuma na tatattara bayanan sirri na dab da fara aiki domin daƙile barazanar tsaro da ake fama da ita a yankin na Sahel.
Duk da cewa Janar Modi bai sanar da sunan sabuwar rundunar haɗin gwiwar da za a kafa ba, amma ya ce shugabannin sojojin ƙasashen uku sun kammala duk wani shiri da ya dace inda nan da makonni kaɗan suka rage kafin rundunar ta fara aiki.
Haka kuma ministan ya ce aikin kafa wannan rundunar ba wani jan aiki ne a wurinsu ba sakamakon sojojinsu suna da ƙwarewa da jajircewa wurin gudanar da ayyukansu.
Yunƙurin kafa wannan rundunar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar ke samun matsala da ƙungiyar ECOWAS inda suka sanar da ficewa daga ƙungiyar.
Ministan Tsaron na Nijar Janar Salifou Modi ya bayyana cewa a lokacin da ECOWAS ta tasa Nijar gaba, da a ce ƙasashen Burkina Faso da Mali ba su tallafa ba, da an kai musu hari.