Sojojin Operation Fansan Yamma ne suka kashe Aminu a wani samame da suka kai tsakanin 20 zuwa 21 ga Janairun 2025. / Hoto: Operation Fansan Yamma

Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da kashe wani gawurtaccen ɗan bindiga, Aminu Kanawa wanda shi ne mataimakin Bello Turji.

Sojojin Operation Fansan Yamma ne suka kashe Aminu a wani samame da suka kai tsakanin 20 zuwa 21 ga Janairun 2025.

Kashe Aminu Kanawa na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan sojojin na Operation Fansan Yamma sun kashe ɗan Bello Turji a wani samame da sojojin suka kai a Fakai.

A sanarwar da mai magana da yawun rundunar ta Operation Fansan Yamma Laftanal Kanal Abubukar Abdullahi ya fitar, baya ga kashe Kanawa, sojojin sun kuma jikkata wasu daga cikin shaƙiƙan Bello Turji waɗanda suka haɗa da Dosso wanda ƙaninsa ne da kuma Danbokolo wanda makusanci ne ga Bello Turji.

Haka kuma sojojin sun kashe wasu daga cikin kwamandojin Bello Turji waɗanda suka haɗa da Abu Dan Shehu da Jabbi Dogo da Dan Kane da Basiru Yellow da Kabiru Gebe da Bello Buba da Dan Inna Kahon-Saniya-Yafi-Bahaushe.

Haka kuma sojojin sun kashe wasu ‘yan ta’adda 24 da ke cikin sansanin Bello Turji da ke kusa da Gebe da ƙananan hukumomin Isa, da kuma Gidan Rijiya da ke Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara.

TRT Afrika