"Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan Somalia a yaƙin da take yi da ta'addanci," in ji sanarwar./Hoto:OTHER

Hukumomi a Turkiyya sun yi Allah wadai da wani hari da 'yan ta'adda suka kai a Somalia

"Mun yi matuƙar baƙin-ciki bisa kisan mutane tare da jikkata wasu sakamakon harin ta'addanci da aka kai El Dheer," a cewar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ranar Asabar.

Ma'aikatar ta yi addu'ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu, sannan ta miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalansu da gwamnatin Somalia, kana ta yi fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.

"Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan Somalia a yaƙin da take yi da ta'addanci," in ji sanarwar.

Mutum aƙalla 25 suka mutu sannan gommai suka jikkata sakamakon wani harin ta'addanci da aka kai a sansanoni huɗu na sojojin Somalia da ke lardin El Dheer da ke tsakiyar ƙasar, a cewar hukumomi.

TRT World