Shugabannin gwamnatocin mulkin soji na ƙasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun ce ba za su koma ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ba.
Sun bayyana haka ne ranar Asabar a taron da suka gudanar a karon farko na ƙungiyar Sahel Alliance AES a Yamai, babban birnin Nijar.
"Mutanenmu sun juya baya ba tare da waiwaye ba ga ECOWAS," kamar yadda shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya bayyana yayin buɗe taron.
Ya ce ƙasashen sun yanke shawarar kafa wata gamayya da za ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar al'ummominsu ba tare da tsoma bakin ƙasashen waje ba.
''Za mu kafa gamayya ta zaman lafiya da taimakon juna da kuma kawo ci gaba a kan mutunta al'adunmu na Afirka," a cewar Tiani.
A watan Janairu ne Nijar da Mali da Burkina Faso suka fitar da sanarwar haɗin gwiwa ta ficewa daga ƙungiyar ECOWAS nan-take.
“Bayan shekaru 49, jajirtattun al'ummar Burkina Faso da Mali da Nijar cikin nadama tare da nuna rashin jin dadinsu na ganin cewa kungiyar (ECOWAS) ta kauce daga akidar kakanninmu da suka kafata ta kishin Afirka,” kamar yadda suka bayyana a wancan lokacin.
Kasashen wadanda ke fama da matsalar masu ikirarin jihadi da talauci, sun yi ta samun matsaloli da ECOWAS tun bayan da aka yi juyin mulki a Nijar a Yulin bara da kuma na Burkina Faso a 2022 da na Mali a 2020.
Duka shugabannin ƙasashen uku sun zargi ECOWAS da kasancewa ‘yar amshin-shatar Faransa haka kuma ba ta yin abin da ya dace wurin daƙile masu iƙirarin jihadi.
A baya dai ECOWAS ta dakatar da duka ƙasashen uku daga cikinta saboda kasancewarsu a ƙarƙashin mulkin soji sannan ta saka musu takunkumai masu tsauri.
Tun a ranar Juma’a da yammaci Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore ya isa Niamey inda ya samu kyakkyawar tarba daga Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani da muƙarrabansa.
Haka kuma Tiani ya karɓi baƙuncin Assimi Goita a ranar Asabar ɗin kafin soma taron.
Tun da farko, fadar shugaban kasar Burkina Faso ta ce "yaƙi da ta'addanci" da "ƙarfafa hadin gwiwa" za su kasance cikin ajandar ranar Asabar, duba da irin munanan hare-haren ta'addanci da kasashen uku ke fuskanta.
Su ma shugabannin na ECOWAS za su yi taro a Nijeriya a ranar Lahadi domin tattaunawa kan dangantakarsu da ƙungiyar ta Sahel Alliance.
A watan Maris ne ƙungiyar ta AES ta sanar da shirinta na yaƙi da masu iƙirarin jihadi, duk da cewa ba ta fito ta bayyana hanyoyin da za ta bi ba.
Haka kuma duka shugabannin ƙasashen uku sun ja layi tsakaninsu da tsohuwar uwar goyonsu wato Faransa inda suka kori sojojinta da ke zaune a ƙasashen inda suka ƙulla ƙawance da Rasha.
Ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun shafe shekaru sun fuskantar hare-haren ta’addanci musamman a yankin da ƙasashen uku suke da iyaka, inda ƙungiyoyin da ke da alaƙa da IS ke kashe farar hula da kai hari ga sojoji inda suke raba miliyoyin jama’a da muhallansu.