'Yan ci-rani kimanin 90 ne suka rasu a kan hanyarsu ta zuwa Turai a lokacin da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a farkon makon nan a gabar tekun Mauritania, in ji kafar watsa labarai ta kasar wadda ta ambato jami'ai na bayani a ranar Alhamis. Ana kuma ci gaba da neman da dama da suka bata.
"Jami'an tsaron teku na Mauritania sun gano gawawwakin mutane 89 da suka hau wani babban jirgin ruwan masunta da ya kife a ranar Litinin 1 ga Yuli a gabar tekun Atlantika," kusan nisan kilomita hudu daga gabar garin Ndiago a kudu maso-yammacin kasar, in ji kamfanin dillancin labarai na Mauritania a ranar Alhamis.
Jami'an tsaron iyakokin tekun sun kuma kubutar da wasu mutanen tara, ciki har da wata yarinya 'yar shekara biyar, in ji kafar yada labaran.
Kamfanin dillancin labaran ya rawaito cewa wadanda suka kubuta na cewa jirgin nasu ya taso ne daga iyakar Senegal da Gambia dauke da fasinja 170, wanda hakan ya sanya ake neman mutane 72 da suka bata.
Hanya mai hatsari
Wani babban jami'in karamar hukuma a yankin da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar wa AFP aukuwar lamarin.
Hanyar tekun Atlantika na da hatsari sosai saboda manyan igiyar ruwa, kuma 'yan ci-rani na yin lodin da ya haura ka'ida a jiragen ruwa, a mafi yawan lokuta jiragen ba su da ingancin shiga teku, kuma ba sa daukar isassen ruwan sha.
Amma hakan ya sake fitowa fili ne sakamakon yadda ake kara sanya idanu kan tekun Bahar Rum.
A shekarar 2023 adadin 'yan ci-rani da suke zuwa tsibiran Canary na Sifaniya ya ninka a shekara guda, wanda ya kai mutane 39,910, kamar yadda gwamnatin Sifaniya ta bayyana.
Mutuwar 'yan ci-rani da yawa
Tsibiran Canary na Sifaniya na daura da iyakar tekun arewacin Afirka da nisan kilomita 100.
Amma jiragen ruwa da dama - mafi yawansu na katako - na kama hanya daga Maroko, Yammacin Sahara, Mauritania, Gambia da Senegal don zuwa tsibiran na Sifaniya.
Sama da 'yan ci-rani 5,000 ne suka mutu a teku yayin kokarin tsallaka wa Sifaniya a watanni biyar na farkon wannan shekarar, ke nan mutane 33 ne ke mutuwa kowacce rana, kamar yadda Caminando Fronteras, wata kungiyar bayar da agaji ta Sifaniya ta bayyana.
Wannan ne adadin rasa rayuka mafi yawa tun bayan da kungiyar ta fara tattara bayanai a 2007, kuma mafi yawa na mutuwa ne a hanyar tekun Atlantika.