Wata majiya ta ce an gano gawar mutum guda yayin aikin ceton./Hoto: Reuters

Sojojin ruwan Maroko sun ceto 'yan ci-rani da 'yan gudun hijira fiye da 800 daga farkon makon jiya zuwa Litinin din da ta wuce yayin da suke yunkurin tsallaka tekun kasar zuwa Sifaniya, a cewar kafofin watsa labaran kasar.

Kafar watsa labaran gwamnatin Maroko MAP, ta ambato wasu majiyoyi ranar Talata suna cewa sojojin ruwan kasar sun ceto 'yan ci-rani da 'yan gudun hijira 845, galibinsu wadanda suka fito daga kasashen Afirka kudu da Sahara, tsakanin 10 ga watan Yuli zuwa ranar Litinin, daga cikin tekun da ke kudancin kasar.

Wata majiya ta ce an gano gawar mutum guda yayin aikin ceton.

Maroko tana arewa maso yammacin Afirka, yankin da ya zama wata hanya ta masu neman mafaka da ke kokarin shiga Turai daga Afirka, inda suke bi ta Sifaniya ko kuma Tsibirin Canary da ke Atlantik.

Tsibirin Canary na Sifaniya yana da nisan kilomita 150 ne kacal daga kudancin Maroko.

Tsibiran Sifaniya sun dade da zama wani wurin wucin-gadi da 'yan ci-rani da kuma 'yan gudun hijira suke isa don shiga kwale-kwalen da za su kai su Turai domin samun rayuwa mai inganci.

Sai dai hanyar da ke hada Atlantik zuwa Tsibiran Canary tana da matukar hatsari inda a yawancin lokuta 'yan ci-rani ke nutsewa a cikin teku.

Kifewar kwale-kwale a Yammacin Sahara

Ranar Talata kungiyar AlarmPhone da ke sanya ido kan 'yan ci-rani da ke neman agajin gaggawa ta wallafa sakon Twitter cewa "mutum 24 sun mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale" a yankin Yammacin Sahara da ake ce-ce-ku-ce a kansa.

Kwale-kwalen, wanda ya kife kwana biyu da suka gabata, yana dauke da mutum 61, ko da yake mutum 37 sun tsira, a cewar kungiyar.

Hukumomin Maroko ba su tabbatar da wannan labari ba.

A makon jiya jami'an kula da teku na Sifaniya sun rika neman kwale-kwale uku dauke da kusan 'yan ci-rani 300 da rahotanni suka ce sun bata, a cewar kungiyar Caminando Fronteras da ke taimaka wa 'yan ci-rani.

AFP