Kawo yanzu dai ofishin jakadancin Romaniya ba ta yi tsokaci kan batun ba

Daga Emmanuel Onyango

An zargi jakadan Romaniya a Kenya Dragos Viorel Tigau kan amfani da kalaman nuna wariyar launin fata a lokacin wani taron wata kungiyar Gabashin Turai inda ya kira takwarorinsa na Afirka ‘birai’.

Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wajen Kenya Macharia Kamau ya ce ba za a lamunci irin wadannan kalaman a ba kowane lokaci, balle karni na 21 a Nairobi.

A wani sakon da ya wallafa ashafinsa na Twitter, Kamau ya soki abin da ya kira kokarin rufa-rufa kan lamarin.

"Hankalina ya tashi kuma raina ya baci bayan da na ji kalaman da jakadan Romaniya a Nairobi ya fada a lokacin da yake magana kan takwarorinsa na Afirka yayin taron kungiyar Gabashin Turai.

"Babban abin kunya ne kokarin yin rufa-rufa kan wannan abin kunyar," in ji shi.

Jakadan da ofishin jakadancin Romaniya ba su yi tsokaci kan zargin ba.

Babu tabbaci kan wurin da ko kuma lokacin da lamarin ya faru.

Lamarin ya biyo bayan jerin takaddamar diflomasiyya kan kalaman jami’an diflomasiyyar kasashen yamma da ake ganin kalamai ne na wariyar launin fata kan ‘yan Afirka.

A watan Janairu, Ma’aikatar Harkokin Wajen Jamus ta nemi afuwa bayan ta yi amfani da alamar damisa wajen bayyana ziyarar Ministan Harkokin Wajen Rasha zuwa Afirka.

Ta wallafa wani sako a shafin Twitter cewar ziyarar Sergey Lavrov ba ta neman damisa ba, amma ziyara ce ta kokarin gamsarwa game da yakin Rasha kan Yukrain.

Wani jami’in Kungiyar Tarayyar Afirka da kuma masu amfani da shafukan zumunta a nahiyar sun nuna bacin rai kan yadda aka siffanta Afirka tamkar wurin zuwa kallon namun daji kawai.

TRT Afrika