A ranar Lahadi ne sojojin Amurka za su kammala janye ma’aikatansu daga sansanin sojin saman Niger 101 da ke babban birnin kasar, sannan su karkata akalarsu wajen ficewa daga wani babban sansanin jirage marasa matuƙa a makonni masu zuwa, in ji wani Janar na Amurka a ranar Juma’a.
A watan Afrilu ne gwamnatin Nijar ta umarci Amurka da ta janye sojojinta kusan 1,000 daga kasar, a wani lamari da ya zama tamkar gwasalewa da bai wa Amurka kunya, bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a bara.
Kafin juyin mulkin, Nijar ta kasance babbar abokiyar ƙawance ga Amurka a yaƙin da take yi da masu tayar da ƙayar baya a yankin Sahel na Afirka, wadanda suka kashe dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu.
Washington na neman wani shiri na biyu a Yammacin Afirka amma jami'ai sun yi gargadin cewa tasirin leƙen asirin da Amurka ke yi kan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin da ke ci gaba da faɗaɗa, yana raguwa sosai a yankin.
Manjo Janar Kenneth Ekman na rundunar sojin saman Amurka da ke Nijar domin gudanar da tsara ficewar jami’an, ya ce za a yi bikin kammala ficewar Amurka daga sansanin Air Base 101. Sansanin dai yana kusa da filin jirgin Diori Hamani da ke Yamai babban birnin ƙasar.
"Za mu yi wani biki na hadin gwiwa a wannan lokacin don kammala kwashe jami’anmu a lokacin da jirgi na ƙarshe na US C-17 zai tashi. Gwamnatin Nijar za ta karɓe iko da tsoffin yankuna da wurare da Amurka ta yi amfani da su," in ji Ekman, yayin da yake magana ta wani taron bidiyo.
Yayin da Amurka ke ficewa, Rasha kuma ta tura dakaru da dama a sansani guda a Nijar, inda suke gudanar da ayyukan horarwa.
Jami’an Amurka sun ce babu wata tuntuɓar juna tsakanin jami’an Amurka da na Rasha a wurin, kuma Ekman ya jaddada cewa ya samu tabbacin cewa ba za a haɗa sojojin a waje ɗaya ba.
“Lokaci na ƙarshe da na yi magana da wani mai magana da yawun Nijeriya, ya ce sojojin Rasha da ke Nijar ba su haura 100 ba.
Kuma ya ce sun gaya masa cewa da zarar sojojin Rasha sun gama horarwar to za a sallame su su koma.