Turkiyya ta damu game da yarjejeniyar da Ethiopia da Somaliland suka kulla

Turkiyya ta damu game da yarjejeniyar da Ethiopia da Somaliland suka kulla

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana ci gaba da goyon baya da kare martabar 'yancin iyakokin Somalia.
Ma'aikatar Harkokin Wajen ta ce "wannan yanayi na bayyana wajabcin, kamar yadda yake a baya, a warware takaddamar da ke tsakanin Somalia da Somaliland ta hanyar tattaunawa kai-tsaye, kuma hakan zai sasanta 'yan Somaliya." Hoto: TRT World

Bayan wata yarjejeniya da Ethiopia da Somaliland suka kulla wadda za ta bai wa Ethiopia damar amfani da tashar jiragen ruwan Somaliland da ke Tekun Maliya, Turkiyya ta fitar da sanarwar goyon baya da kare martabar iyakokin Somalia.

"Yarjejeniyar Fahimtar Juna don Hadin Kai da Aiki Tare da aka sanya hannu a kai a Addis Ababa a ranar 1 ga Janairu, 2024 tsakanin Jamhuriyar Ethiopia da Somaliland, ba tare da sani da yardar gwamnatin Somalia ba, na sanya damuwa," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a wata sanarwa da ta fitar.

Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed da Shugaban Kasar Somaliland Muse Bihi Abdi ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Litinin.

Bayan kulla yarjejeniyar, Turkiyya ta bayyana goyon bayanta ga hadin kai, 'yancin mulki da kare martabar iyakokin Tarayyar Jamhuriyar Somalia, kamar yadda yake kunshe a wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar a ranar Alhamis din nan, tana mai jaddada muhimmanci aiki da dokokin kasa da kasa kan wannan batu.

Ethiopia da ba ta da iyaka da teku ta sanya hannu da yankin Somaliland da ya balle daga Somalia, don amfani da Tashar Jiragen Ruwa ta Berbera.

A wani bangare na yarjejeniyar, Somaliland ta shirya bayar da fili a tsandauri mai nisan kilomita 20 ga Ethiopia don kafa sansanin sojin ruwa, in ji Abdi a wajen sanya hannun.

Ma'aikatar Harkokin Wajen ta ce "wannan yanayi na bayyana wajabcin, kamar yadda yake a baya, a warware takaddamar da ke tsakanin Somalia da Somaliland ta hanyar tattaunawa kai-tsaye, kuma hakan zai sasanta 'yan Somaliya."

Sanarwar ta kara da cewa "Muna sabunta goyon baya ga duk wani yunkuri da zai kawo wannan tattaunawa."

Yankin Somaliland ya balle daga Somalia sama da shekaru 30 da suka gabata, amma har yanzu Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya ba su amince da 'yancinsa ba. Har yanzu Somalia na yi wa Somaliland kallon wani bangare nata.

TRT World