Akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin Turkiyya da Nijar. Hoto/@TCNiameyBE

Jakadan kasar Turkiyya a Nijar Ozgur Cinar ya jagoranci wata tawagar ‘yan kasar Turkiyya da ke ziyarar aiki a kasar inda suka kai wa Ministan tsaron Nijar, Malam Alkassoun Indattou ziyara.

A yayin wannan ganawar, sun tattauna a kan batutuwa da dama musamman wadanda suka shafi tsaro.

Tawagar ta kasar Turkiyya ta je Nijar din ne domin halartar zaman taro na biyu domin kara lalubo wasu sabbin hanyoyi na kara karfafa huldar kamfanoni da masana’antu na fannin harkokin tsaro.

Turkiyya da Nijar din sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama musamman a bangaren soji da sauran fannoni na jami’an tsaro da horo ta hanyar amfani da ilimin kimiyyar zamani.

Wannan duk wani yunkuri ne na kara yaukaka dangantaka ko kuma hulda tsakanin kasar ta Nijar da Turkiyya.

Ko a kwanakin baya sai da Turkiyyar ta sayar wa Nijar din makamai da jirage marasa matuka domin kara inganta tsaron kasar.

Nijar na fama da barazanar masu ikirarin jihadi da ke kai hare-hare a Yammacin Afirka da suka hada da kungiyoyin Boko Haram da Iswap.

TRT Afrika da abokan hulda