Rikicin Sudan ya yi kamari yayin da Amurka da Saudiyya suka sabunta kira a tsagaita wuta

Rikicin Sudan ya yi kamari yayin da Amurka da Saudiyya suka sabunta kira a tsagaita wuta

An kashe fiye da mutum 1,800 a rikicin da aka kwashe fiye da mako bakwai ana yi wanda babu alamar kawo karshensa.
Hotunan wasu motoci da aka cinna wa wuta a hedikwatar Hukumar Kasafi ta Sudan da ke kan titin al-Sittin a kudancin Khartoum ranar 29 ga watan Mayun 2023. / Hoto: AFP

Amurka da Saudiyya sun sake sabon yunkuri na yin sulhu tsakanin janar-janar da ke fafatawa da juna a rikicin da aka shiga mako na takwas ana gwabzawa a Sudan.

Masu shiga tsakani na kasashen waje sun yi kira ga "bangarorin biyu su amince su aiwatar da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta, da zummar samar da wata tartibiyar hanya ta magance rikicin", kamar yadda Riyadh ta bayyana ranar Lahadi.

Ranar Asabar da maraice yarjejeniyar tsagaita wutar da aka tsawaita sakamakon shiga tsakanin da Amurka da Saudiyya suka yi ta kare, ba tare da alamar daina rikicin ba.

Bangarorin biyu sun yi fatali da yarjeniyoyin tsagaita wuta da dama da suka kulla a baya kuma hakan ya sa Washington ta sanya musu takunkumai ranar Alhamis, bayan ta zarge su da laifin "gagarumin" zubar da jini.

Har yanzu wakilan rundunar sojin Sudan da na dakarun rundunar Rapid Support Forces (RSF) suna birnin Jeddah na Saudiyya duk da cewa yarjeniyoyin da suka kulla na tsagaita wuta a baya ba su yi tasiri ba, a cewar ma'aikatar wajen kasar.

Ranar Lahadi rundunar RSF ta yi ikirarin cewa ta harbo wani jirgin yaki bayan sojoji sun "kaddamar da gagarumin hari ta sama kan wuraren da dakarunmu suke" a arewacin Khartoum.

Wata majiyar soji ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wani jirgin yaki kirar China ya yi hatsari a kusa da sansanin Wadi Seidna da ke arewacin Khartoum sakamakon "tangardar na'ura".

Ganau sun ce sun hangi wani jirgi yana tafiya daga kudanci zuwa arewacin babban birnin yana ci da wuta.

Alkaluman cibiyar tattara bayanai kan rikice-rikice ta Armed Conflict Location and Event Data Project sun ce an kashe fiye da mutum 1,800 a Sudan yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan 1.2 sun rasa matsugunansu, kana fiye da mutum 425,000 suka tsere kasashen waje.

TRT World