Rundunar sojin ruwan Nijeriya sun yi yarjejeniya da Turkiyya don inganta jirgin yakinta

Rundunar sojin ruwan Nijeriya sun yi yarjejeniya da Turkiyya don inganta jirgin yakinta

Tun shekarar 1985 aka kaddamar da NNS ARADU a Rundunar Sojin Ruwan Nijeriya.
Turkiyya da Nijeriya na kulla yarjeniyoyi a fannoni daban-daban/ Hoto: @turkdegs

Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya ta sanya hannu kan yarjejeniya da wani kamfanin kera jiragen ruwa na Turkiyya ‘Dearsan Shipyard‘ don inganta jirgin ruwan yakinta mai suna NNS ARADU.

Shugaban Rundunar Sojin Ruwan Nijeriya Vice Admiral Awwal Gambo a ranar Talatar nan ya bayyana cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar da manufar inganta ayyukan tsaron rundunar ruwan Nijeriya a iyakokin teku da take da iko da su.

Gambo ya kuma ce a shekarar 1985 aka kaddamar da NNS ARADU a Rundunar Sojin Ruwan Nijeriya, kuma shi ne jirgin ruwan yakinta mafi girma da muhimmanci a kasar.

Jirgin ya wakilci Nijeriya a ayyukan sojojin ruwa da yawa a Afirka da ma wajen nahiyar.

Ya kara da cewa “Wani abu mai muhimmanci a wannan rana kuma shi ne yadda aka sanya hannu kan kawo karin jirgin yaki na ruwa samfurin ‘Fast Attack Craft’ mai tsayin mita 57 don taimakawa wajen ayyukan sake fasali da inganta NNS ARADU”.

Ya ce “Babu shakka tabbatar da ayyukan wadannan jiragen ruwa biyu ba adadin jiragen ruwan zai kara ba kawai, zai kuma daga martabar Rundunar Sojin Ruwan Nijeriya wajen ayyukan tsaron teku a Afirka da wajen ta.”

Ya ci gaba da cewa an zabi kamfanin na Turkiyya saboda irin nasarorin da kamfanin ya samu wajen kera jiragen ruwan yaki masu inganci, sannan yana cika alkawarin da aka kulla da shi.

Ya kuma ce a yanzu haka kamfanin na ‘Dearsan Shipyard’ na aikin samarwa da Nijeriya jiragen ruwan sintiri guda biyu a Turkiyya.

jami'an Nijeriya a Turkiyya yayin sanya hannu kan yarjejeniyar samar OPV a 2021/ Hoto: @turkdegs 

Ya ce “Wannan yarjejeniya za ta inganta alakar bangarorin biyu tare da karfafa tsaro da kuma ayyukan samar da jiragen yaki za su taimaaka wajen cimma burin Nijeriya na ci-gaba mai dorewa.”

A nasa jawabin, shugaban sashen tsara manufofi na Rundunar Sojin Nijeriya Rear Admiral Saidu Garba, ya bayyana cewa jirgin ruwan mai tsayin mita 125.6 ne mafi girma a Rundunarsu.

Garba ya kara da cewa NNS ARADU jirgi ne da ke iya yin dukkan wani aiki na yaki a teku tare da hadin kai da sauran bangarori.

Ya ce jirgin ya yi yawo na mil 6,500 inda ya bayar da taimakon yaki ga dakaru abokai a gabar teku.

NNS ARADU/ Photo: NTA

Ya kuma ce “Tun lokacin da muka shiga aikin soja jirgin yake halartar ayyukan sojin ruwa a yankuna daban-daban.

Ya je ayyukan diflomasiyya a kasashen Gabon da Congo da Zaire Equitorial Ginea da ma kasashen Turai da dama.”

Manajan Darakta na kamfanin ‘Dearsan Shipyard’ Murat Gordi ya godewa Rundunar Sojin Ruwan Nijeriya saboda aikin daga martaba da inganta jirgin ruwan yaki na NNS ARADU da ta ba su.

Ya yi alkawarin za su kammala wannan aiki a kan kari kuma cikin inganci, inda ya kara da cewar alakarsu da Nijeriya ta faro tun 2021 a lokacin da aka ba su aikin samar da jiragen ruwa na OPV masu tsayin mita 76.

TRT Afrika da abokan hulda