Jami'an sojin saman Nijeriya sun iso Ankara, babban birnin Turkiyya. / HotoTwitter/ @NigAirForce

Jami’an sojin saman Nijeriya sun iso birnin Ankara na Turkiyya don samun horo kan amfani da jiragen sama kirar Turkiyya.

Ma’aikatar Sararin Samaniyar Turkiyya ce ke kera jiragen masu saukar ungulu samfurin T129 ATAK.

Kakakin rundunar sojin sama ta Nijeriya, Air Commodore Ayodele Famuyiwa ne ya sanar da wannan labari.

A bara ne gwamnatin Nijeriya ta shiga yarjejeniya da Turkiyya don kerawa da samar da jirage shida samfurin T129 masu saukar angulu. Nijeriya na bukatar jiragen ne saboda yakar ‘yan ta’adda da suka addabi kasar.

Jiragen masu saukar angulu na T129 ATAK suna da inji biyu, da kujerun matuka biyu. Kuma jiragen yaki ne da ake amfani da su wajen ayyuka daban-daban, sannan suna iya aiki a ko wane yanayin samaniya.

Kashi na farko na sojojin matuka jirgin sama, tare da injiniyoyi za su samu horo kan amfani da jirage masu saukar angulu na T-129 ATAK, wadanda Nijeriya ta shiga yarjejeniya siya daga Hukumar Kera Jiragen Sama na Turkiyya. Adadin da jami’an suka bayyan ya kai 26.

Ana sa ran za a mika jiragen ga sojin Nijeriya kafin tsakiyar wannan shekara ta 2023.

Da ma tun a shekarar 2022 aka jiyo kwamandan rundunar sojin saman Nijeriya, Chief of Air Staff, Air Marshal Oladayo Amao yana bayar da haske kan siyo jiragen daga Turkiyya.

Jiragen da kwamandan ya ambata sun hada da jirgin soji na daukar kaya samdufin CASA-295, guda biyu. Sai kuma samfurin Beechcraft King Air 360, guda biyu.

Sannan da jirgin rangadi samfurin Diamond DA-62 guda hudu. Sai samfurin Wing Loong II UCAV, guda 3, da kuma T-129 ATAK guda shida.

TRT Afrika