Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba shi da niyyar mayar da Legas babban birnin Nijeriya daga Abuja.
Mai bai wa shugaban kasar shawara kan watsa labarai da tsare-tsare Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafin X.
“An soma watsa wannan jita-jitar a lokacin yaƙin neman zabe a bara inda ƴan adawa ke neman duk wasu hanyoyi na daƙile shi,” in ji sanarwar.
Ya bayyana cewa masu watsa irin waɗannan labaran ba su da gaskiya sannan ya bayyana cewa su ne gaba-gaba wurin nuna kabilanci a kasar.
“Mayar da FAAN Legas, wanda sashe ne a ƙarƙshin Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama, wanda a can yake kafin tsohon minista Hadi Sirika ya mayar da shi Abuja a gwamnatin baya, ba shi ke nufin za a mayar da babban birnin Nijeriya Legas ba.”
Haka kuma ya bayyana cewa bai kamata a razana da mayar da wani sashe na Babban Bankin Nijeriya zuwa Legas ba sakamakon akasarin bankunan kasar hedikwatarsu tana Legas.
Ya kuma bayar da misali kan cewa akwai ma’aikatun gwamnatin Nijeriya da hedikwatarsu ba a Abuja take ba, wadanda suka hada da NIMASA da NPA ke Legas haka kuma akwai NIWA da ke Lokoja.