Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja da ke Nijeriya ta saki yaran nan guda 26 a ranar Talata, wadanda aka zarga da kuma tuhumarsu da cin amanar ƙasa, bayan umarnin sakin nasu da Shugaba Bla Ahmed Tinubu ya bayar.
An kama "ƙananan yaran" ne a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a watan Agusta bayan da aka zarge su da ɗaga tutocin ƙasar Rasha.
An miƙa yaran 26 tare da sauran manya fiye 50 ga ma'aikatar jinƙai bayan sakin nasu.
Alƙalin Kotun, Mai Shari'a Obiora Egwuatu, a ranar Talata ya soke ƙarar bayan M. D Abubakar, lauyan Antoni Janar na Nijeriya ya shigar da buƙatar yin hakan.
Umarnin na shugaban Nijeriya na zuwa ne bayan an gurfanar da yaran a gaban kotu a makon jiya, lamarin da ya jawo zazzafan martani daga ɓangarori daban-daban a faɗin ƙasar.
Tun da fari a ranar Litinin Ministan Watsa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris ya shaida wa manema labarai kan cewa Shugaba Tinubun ya bayar da umarnin a gaggauta sakin yaran ba tare da la'akari da duk wata shari'a da suke fuskanta ba.
Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa Antoni Janar na ƙasar, Lateef Fagbemi, damar janye ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar a gaban kotu ta hanyar karɓe lamarin daga hannun Babban Sufeton Rundunar 'Yan sanda.
Daga nan ne Mai Shari'a Egwuatu ya soke ƙarar abin da ke nufin an wanke mutum 119 daga zargin da gwamnati ta yi musu na cin amanar ƙasa.
Ko da yake mutanen ba su bayyana a gaban kotun ba, alƙalin ya yi umarni a sake su daga gidan yari nan-take.