A baya dai Shugaban Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo ya ayyana 24 ga watan Nuwamban shekarar 2024 a matsayin ranar zabukan kasar bayan ya dakatar da majalisar dokokin kasar a watan Disamban shekarar 2023. / Hoto: Reuters / Photo: AFP

Shugaban Guinea-Bissau ya ɗaga zaɓukan majalisar dokokin ƙasar da za a yi ranar 24 ga watan Nuwamba har sai baba ta gani, lamarin da ya tsawaita rashin tabbas a fagen siyasar ƙaramar ƙasar ta Yammacin Afirka.

A baya dai Umaro Sissoco Embalo ya ayyana ranar 24 ga watan Nuwamba a matsayin ranar zaɓukan bayan ya rusa majalisar dokokin ƙasar a wani martani ga abin da ya kira wani yunƙurin juyin mulki.

Amma tun makon jiya ne aka fara tsammanin za a ɗaga zaɓukan domin rashin zaman lafiya da ake fama da shi a ƙasar mai amfani da harshen Portugal.

Ranar ɗaya ga watan Nuwamba, ministan cikin gida, Aristides Ocante da Silva, ya yi gargaɗin cewa cigaba da zaɓen zai yi wuya domin matsaloli na gudanarwa da kuma rashin kuɗi.

Soke dokar watan Yuli

Embalo kuma ya bayyana ranar Lahadi cewa shi zai ɗaga zaɓen a hukumance cikin wannan makon.

A ranar Litinin ne dai shugaban ya soke dokar watan Yulin shekarar 2024 da ta saka wannan watan a matsayin watan zaɓukan, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin siyasa Fernando Delfim da Silva ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Bissau.

Sai dai kuma Embalo bai tsayar da sabuwar ranar zaɓe ba, kuma Silva ya ce za a ayyana jadawalin zaɓen ne a wata doka da za a fitar nan gaba.

Rashin tabbas da ke tattare da zaɓukan ‘yan majalisun dokokin ƙasar na kusan iri ɗaya ne da rashin tabbas da ke tattare da zaɓen maye gurbin Embalo a matsayin shugaban ƙasa.

Fama da juyin mulki

Wani ƙawancen jam’iyyu a ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar PAIGC, ya daɗe yana adawa da shugaban kuma ya kasance mai rinjaye a majalisar dokokin ƙasar tun watan Yunin shekarar 2023.

Wannan ya tilasta wa Embalo kasancewa tare da shugaban PAIGC cikin wani yanayi na takun-saƙa, wani lamarin da ya hargitsa yiwuwar gudanar da sabbin zaɓuka.

Bugu da ƙari Guinea-Bissau na shan wahalar samun kuɗin da za ta gudanar da zaɓuka.

Tun lokacin da ta samu ‘yancin kai daga ƙasar Portugal, ƙasar ta yi fama da juyin mulki da dama.

Tafarkin Dimokuraɗiyya

Duk da cewa Guinea-Bissau ta koma tafarkin Dimokuraɗiyya cikin shekaru goma da suka wuce, ta ci gaba da fuskantar hatgitsin siyasa.

Dambarwar siyasar ta ci gaba bayan an zaɓi Embalo a watan Disamban shekarar 2019 a wa’adin shekara biyar, yayin da wa’adin zaɓen da kuma lokacin zaɓen shugaban ƙasa na gaba ke cike da gardama

TRT Afrika