Gwamnatin Kano ta yi watsi da rahotannin da ake yaɗawa kan cewa akwai rashin jituwa tsakanin Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf da kuma jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A ranar Litinin ne jaridar Daily Nigerian a ƙasar ta fitar da wani labari wanda ke zargin cewa gwamnan na Kano da daina ɗaukar wayar uban gidansa wato Rabiu Kwankwaso, lamarin da ta tayar da ƙura a kafofin sada zumunta.
Sai dai a wata sanarwa da babban mai taimaka wa gwamnan Kano kan kafofin sada zumunta Salisu Yahaya Hotoro ya fitar, babu wata rashin jituwa tsakanin Abba da mai gidan nasa Kwankwaso.
“Wannan zargin ba gaskiya bane kuma karkatar da hankali ne sakamakon Gwamna Abba yana da ladabi da alaƙa mai kyau da Rabiu Kwankwaso, inda yake kallonsa a matsayin jagora a jam’iyya da kuma tafiyarsa ta siyasa. Duk wata magana ta ɓaraka a tsakaninsu ba wai batu ne kawai na zuzutawa ba, amma ya saɓa wa mu’amularsu ta aiki,” in ji sanarwar.
“Gwamna Abba K Yusuf ya himmatu sosai wajen tabbatar da akidu da hangen nesa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP). Ya himmatu wajen samar da hadin kai a cikin jam’iyyar tare da yin aiki tare da dukkan ‘ya’yan jam’iyyar ciki har da Kwankwaso domin cim ma burinmu,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.
A ‘yan kwanakin nan ana ta samun raɗe-raɗin rashin jituwa a tsakanin gwamnan na Kano da kuma Kwankwaso inda har wasu da ba a tabbatar da ko su wane ne ba suka fitar da wata tafiya mai suna Abba Tsaya da Kafarka, wadda ke nufin Abban ya ƙaurace wa Kwankwaso.
Da farko an zargin sakataren gwamnatin Abdullahi Baffa Bichi da assasa tafiyar sai dai ya fito ya kare kansa daga wannan zargin.