Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta sakin ƙananan yaran ba tare da la'akari da duk wata shari'a da suke fuskanta ba, kamar yadda ministan watsa labarai na Nijeriya ya tabbatar.
Umarnin na shugaban Nijeriyar na zuwa ne bayan an gurfanar da yaran a gaban kotu a makon da ya gabata, lamarin da ya jawo zazzafan martani daga ɓangarori daban-daban a faɗin ƙasar.
Ministan Watsa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris a ranar Litinin ya shaida wa manema labarai kan cewa Shugaba Tinubun ya bayar da umarnin a gaggauta sakin yaran ba tare da la'akari da duk wata shari'a da suke fuskanta ba.
Shugaban ya kuma umurci ma’aikatar jin kai da rage radadin talauci da ta gaggauta duba lafiyar wadannan yara kanana, sannan kuma ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin sun hadu da iyayensu ko masu kula da su a duk inda suke a kasar.
Shugaba Tinubun ya kuma ba da umarnin a kafa wani kwamiti wanda ma’aikatar kula da jin kai za ta jagoranta domin duba duk wasu batutuwan da suka shafi kamawa, tsare su, kulawa da kuma sakin yaran.
An kama "ƙananan yaran" ne a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a watan Agusta bayan da aka zarge su da ɗaga tutocin ƙasar Rasha a lokacin.