Dakarun Wanzar da Zaman Lafiya na Riƙo na Tarayyar Afirka AU a Somalia (ATMIS) sun kammala miƙa sansanonin soja 21 ga sojojin Somalia, abin da ya kawo ƙarshen janyewar ta matakai uku ta dakarun a hukumance, kamar yadda shirin wanzar da zaman lafiyar ya bayyana a ranar Alhamis.
Shirin na wanzar da zaman lafiya ya janye jumullar sojoji 9,000 daga Somalia a shirye-shiryen wani sabon shirin tura dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya ke goya wa baya a ƙasar.
Sansanin Burgavo Forward a jihar Jubaland shi ne “sansani na ƙarshe da aka miƙa wa Rundunar Sojan Somalia,” kamar yadda shirin wanzar da zaman lafiyar ya bayyana a cikin wata sanarwa, yana bayani a kan sansanin dake yankin kudanci, kilomita 530 daga babban birnin ƙasar, Mogadishu.
Sansanin, Sojojin Kenya ne suka yi iko da shi, kuma “ya taka muhimmiyar rawa wajen dakushe tasirin Al-Shabab da kuma tsare babbar hanyar jigila ta Burgavo-Ras Kamboni,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sabon shirin wanzar da zaman lafiya
Sabon shirin na AU na tallafi da daidaita al’amura a Somalia wanda zai maye gurbin na yanzu, zai fara aiki ne a Janairu kamar yadda aka tsara.
Miƙa sansanonin na nuna gagarumin mataki na yadda Somalia ke ɗaukan alhakin tsaronta baki ɗaya, matakin da ya zo a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rikici tsakanin ƙabilu da kuma ƙalubalen da sauyin yanayi ya kawo.
Majalisar Dinkin Duniya ta ba da rahoton cewa tashin hankalin da ake fuskanta a tsakanin ƙabilu a arewaci da tsakiya da kudancin Somalia, wanda ya samo asali daga rikici kan filayen kiwo, ya raba dubban mutane da mahallansu, ya kuma yi mummunan tasiri kan raywar yau da kullum a yankunan.
Ƙari a kan haka, har yanzu damina ba ta fadi ba a yankuna da dama, saɓanin yadda ake sa rai, inda a bisa al’ada ake shiga damina a watan Oktoba kuma ake ci gaba da ruwa har zuwa ƙarshen shekara.