Somalia ta kori jakadan Ethiopia daga kasar a ranar Alhamis, ta kuma rufe ofisoshin jakadancin kasar biyu a yankin Puntland mai cin gashin kai, da kuma wani ofishin a yankin Somaliland da ya balle, sakamakon rikici kan tashar jiragen ruwa, in jami'an gwamnatin Somalia.
Ethiopia ta amince da wata yarjejeniya ta amfani da yanki mai nisan kilomita 20 a gabar tekun Somaliland - yankin da Somalia take ikirarin nata ne, duk da cewa yankin na arewaci na jin dadin cin gashin kansa tun 1991.
Ethiopia ta ce tana son kafa sansanin sojin ruwa, ita kuma ta biya hakan da amincewa da 'yantacciyar kasar Somaliland - wanda hakan ya sanya Somalia mayar da martani.
Ana tsoron hakan zai ci gaba da dagula al'amuran tsaro a yankin Kahon Afirka.
A watan Fabrairu, Shugaban Kasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya ce kasarsa 'za ta kare kanta" idan har Ethiopia ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar.