Rikici ya kara kamari a babban birnin Sudan Khartoum a jajibirin Babbar Sallah bayan da kungiyar RSF ta kwace iko da babban sansanin ‘yan sanda na birnin.
Rikicin da ake yi tsakanin sojojin Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al Burhan da kuma jagoran RSF Mohamed Hamdan Dagalo ya fi mayar da hankali ne a kan sansanonin sojoji.
Hakazalika a yammacin Sudan, rikici na kara kazancewa a yankin Darfur kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar.
Tun bayan da rikici ya barke a ranar 15 ga watan Afrilu, RSF ta kafa sansanoni a ungwanni da dama da jama’a ke zaune a babban birnin, inda sojojin kasar ke ta gwagwarmaya wurin samun gindin zama a kasa duk da karfin da suke da shi ta sama.
A daidai lokacin da RSF din ke kokarin kwace duka Khartoum, miliyoyin mutane na ta kokarin guduwa duk da an saka su tsaka mai wuya sakamakon musayar wutar da ake yi ga kuma rashin lantarki da ruwa a daidai lokacin da ake tsananin zafi.
A daren Lahadi, RSF ta sanar da cewa ta kwace iko da babbar hedikwatar ‘yan sanda da ke kusurwar kudancin Khartoum wadda Amurka ta saka wa takunkumi a bara sakamakon take hakkin bil adama.
A ranar Talata, RSF ta kai hari sansanonin soji a tsakiya da arewaci da kudancin Khartoum, kamar yadda shaidu suka bayyana.
Ga Musulmai da dama wadanda ke gwagwarmayar tsira a lokacin yaki, dandanon ragon Sallah wanda ake yankawa ya zama wani abu mai wahala a gare su.
Mawaheb Omar, wadda mahaifiya ce mai ‘ya’ya hudu wadda ta ki yarda ta bar gidanta ta shaida wa AFP cewa Sallar Idi babban lamari ne a Sudan, za ta zama “babu dadi”, sakamakon ko nama ba za ta iya saya ba.
Shugaban sojin Sudan Burhan ya yi jawabi ta talabijin a ranar Talata inda ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar farko ta Idi.
“Makiricin da aka shirya na bukatar kowa ya zama cikin shiri domin mayar da martani kan barazanar waje da ake yi wa kasarmu, da haka muna kira ga duk wani matashi wanda zai iya kare kasarsa da kada ya yi kasa a gwiwa wurin taka wannan rawa, ko daga wurin da yake zama ko kuma shiga aikin soja,” kamar yadda Burhan ya bayyana a lokacin jawabin da ya yi.
Shi ma shugaban RSF Dagalo wanda aka fi sani da Hemetti ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar Talata da Laraba a wani sakon murya bayan da dakarunsa suka kwace iko da babban sansanin ‘yan sanda da ke kudancin Khartoum inda suka kwace gomman motoci da makamai da dama.
Satar kayayyaki
Majalisar Dinkin Duniya da Norway da Birtaniya wadanda aka fi sani da Troika a ranar Talata sun yi tir da “bazuwar take hakkin bil adama da cin zarafi ta hanyar lalata, da kuma bita-da-kulli kan wata kabila a Darfur,” inda akasari aka fi alakantawa da sojojin RSF da kawayensu masu rike da makamai.
RSF sun fito daga tsatson Janjaweed wadanda Khartoum ta fito da su domin dakile rikicin ‘yan tawaye na yankin Darfur a 2003, inda aka yi musu zarge-zarge da laifukan yaki.
A rikicin da ake yi a halin yanzu, ana ta zargin rundunar RSF da satar kayayyakin jin kai, da shiga masana’ntu da gidajen da aka gudu aka bari na wadanda yaki ya daidaita ko kuma aka kwace karfi da yaji.
Dagalo ya mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi musu ta a wani sakon murya wanda aka wallafa ta intanet. “RSF za ta dauki mataki mai tsauri” kan dakarunta wadanda suka gudanar da wannan mummunan cin zarafin, a cewarsa.
A ranar Litinin RSF din ta sanar da cewa ta soma shari’a kan wasu daga cikin dakarunta masu kunnen kashi da kuma sakin wasu daga cikin fursunonin yaki 100 daga cikin sojojin kasar.
Tun da aka soma wannan rikici, duka bangarorin sun sha bayyana cewa sun yi musayar fursunoni da taimakon kungiyar Red Cross, inda ba su taba bayyana ainahin adadin wadanda aka kama ba.