Ana yawan samun hare-haren 'yan bindiga musamman a arewacin Nijeriya. Hoto/Reuters

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa ta kashe ‘yan ta’adda 31 sannan kuma ta kama 81 a Nijeriya a makon da ya gabata.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya Janar Edward Buba ya fitar a ranar Lahadi, sojojin sun kwato mutum goma wadanda ke hannun ‘yan ta’addan.

Sojojin sun ce akwai mayakan Boko Haram 63 wadanda suka yi saranda ga ‘yan sanda duk a makon da ya gabata.

Buba ya ce wadanda aka kama da kuma aka kashe akasarinsu a arewacin kasar ne.

Sojojin sun ce akwai bindigar AK-47 guda 12 da kuma wasu makamai na gargajiya guda biyu da harba ruga uku da kuma harsasai 81 da jigida hudu da babura uku wadanda aka kwato daga hannun ‘yan ta’adda a Borno da Yobe.

Sojojin sun ce akwai wasu mutanen da aka kama a Jihar Benue.

"Sojoji na ci gaba dayin galaba kan ‘yan tayar da kayar baya da ta'addanci tare da manufar tabbatar da tsaron kasa daga masu ta'addanci," in ji Buba.

TRT Afrika