Mista Mahama ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa ta ɓangaren cika alƙawuran da ta ɗauka ga al’ummar Musulmi a lokacin yaƙin neman zaɓe. / Hoto: Ghana Presidency

Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya sanar da shirye-shiryen bayar da ƙarin kwana ɗaya a yayin shagulgulan bikin Ƙaramar Sallah da kuma rage kuɗin Aikin Hajji ga Musulman ƙasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin addu’o’i na musamman da aka gudanar a Babban Masallacin Accra a ranar Juma’a.

Mista Mahama ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa ta ɓangaren cika alƙawuran da ta ɗauka ga al’ummar Musulmi a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Shugaba Mahama ya ce za a yi wannan gyaran na ƙarin hutun Sallah da zarar majalisar dokokin ƙasar ta soma zama.

Idan ƙarin ya tabbata, hakan zai bai wa Musulman Ghana damar samun hutun kwanaki biyu domin gudanar da shagulgulan Ƙaramar Sallah a maimakon kwana guda da suke samu a baya.

Baya ga ƙarin hutun Sallah, Mista Mahama ya kuma sanar da aniyarsa ta rage kuɗin Aikin Hajji inda ya ce ya kafa kwamiti na musamman kan hakan inda kwamitin zai tafi Saudiyya ranar Litinin domin tattauna yiwuwar rage kuɗin Aikin Hajjin.

A ranar 7 ga watan Janairu ne aka rantsar da sabon shugaban ƙasar na Ghana John Dramani Mahama bayan ya lashe zaɓen ƙasar wanda aka gudanar 7 ga watan Disamabar 2024.

Mahama ya maye gurbin Nana Akufo-Addo, wanda ya sauka bayan kammala wa'adi biyu na shugabanci.

TRT Afrika da abokan hulda