Sai dai ta wani ɓangaren kuma wasu daga cikin jama’ar yankin na cewa mutanen da suka rasu sun kai 30.

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce ‘yan bindiga sun kashe ‘yan bijilanti 21 a jihar.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata a ƙauyen Baure da ke Ƙaramar Hukumar Safana yayin da ‘yan bijilantin ke dawowa daga wurin ta’aziyyar wani ɗan ƙungiyar bijilanti ta jihar da ya rasu.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tun bayan samun rahoton lamarin, jami’ansu suka garzaya wurin inda suka kai ɗauki da kuma tabbatar da komai ya lafa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce wasu ‘yan bindiga ne waɗanda suka shahara a yankin na Safana suka kai hari kan ‘yan bijilantin.

Sai dai ta wani ɓangaren kuma wasu daga cikin jama’ar yankin na cewa mutanen da suka rasu sun kai 30.

Haka kuma rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun ƙona wasu gawawwakin sannan kuma ba a ga wasu ba.

TRT Afrika da abokan hulda