Jami'in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Kongo ya bayyana damuwarsa a ranar Juma'a game da ɗumbin mutanen da suka rasa matsugunansu a lardin Kivu ta Arewa sakamakon kazamin fada tsakanin sojoji da 'yan tawaye.
"Tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2025, fiye da mutum 100,000 ne suka rasa matsugunansu a yankin Masisi sakamakon ci gaba da gumurzun da ake yi tsakanin 'yan kungiyar M23 da sojojin Kongo," in ji jami'in a cikin wata sanarwa.
Bruno Lemarquis ya bayyana rashin jin dadinsa game da ci gaba da taɓarɓarewar al'amuran jin kai a Kivu ta Arewa, ya kuma bukaci a mutunta dokokin jin kai na kasa da kasa.
Fiye da mutum miliyan 2.8 sun riga sun yi gudun hijira a Kivu ta Arewa, fiye da kashi ɗaya bisa uku na al'ummar lardin.
Ƙwace gari
A baya-bayan nan ne kungiyar 'yan tawayen M23 ta tsananta rikici a gabashin Kongo inda ta ƙwace wasu muhimman garuruwa kamar su Katale da Masisi wanda hakan ya tilasta wa da dama barin gidajensu.
Akwai ƙungiyoyin ‘yan tawaye da dama da ke aiki a gabashin Kongo, amma ‘yan tawayen M23 wadanda aka ce mayakansu ‘yan kabilar Tutsi ne suka fi shahara.
Sanarwar ta ce tashe-tashen hankulan sun kuma shafi waɗanda ke cikin sansanonin 'yan gudun hijira.
Haka kuma sanarwar ta ce su ma ma’aikatan jin ƙai suna mutuwa sakamakon rikicin inda a bara sai da ma’aikatan jin ƙai tara suka rasu.