Hukumar ba da agajin lafiya ta MSF ta ce a ranar Juma’a an tilasta mata dakatar da ayyukanta a daya daga cikin ‘yan tsirarun asibitocin da ke kudancin Khartoum sakamakon hare-haren da aka kai musu, lamarin da ya katse wata hanyar ceto ga wadanda suka rage a babban birnin na Sudan.
Asibitin, wanda ke cikin yankin da RSF ke iko da shi, ya taimaka wajen kula da wadanda suka jikkata sakamakon hare-hare ta sama da sojojin kasar Sudan suke kai wa akai-akai, da kuma daruruwan mata da kananan yara da ke fama da tamowa a yankin wanda aka ayyanan wasu unguwanninsa biyu a matsayin masu fuskantar barazanar yunwa.
A cikin wata sanarwa da MSF ta fitar ta ce "A cikin watanni 20 da kungiyoyin MSF suka yi aiki tare da ma'aikatan asibiti da masu aikin sa kai, asibitin Bashair ya sha fama da hare-haren mayaka wadanda ke shiga asibitin da makamai da kuma yin barazana ga ma'aikatan lafiya, inda suke bukatar a kula da mayakan wajen yi musu magani kafin sauran marasa lafiya."
"Duk da yawan shiga tsakanin masu ruwa da tsaki, wadannan hare-haren sun ci gaba da faruwa a cikin 'yan watannin nan. Yanzu MSF ta dauki mataki mai matukar wahala na dakatar da dukkan ayyukan jinya a asibitin."
Yakin da ake gwabzawa a Sudan ya dakatar da kashi 80 cikin 100 na ayyukan asibitocin da ke yankunan da ake fama da rikici, inda miliyoyin da ba za su iya tserewa tashe-tashen hankula da ke ci gaba da wanzuwa ba.
Fararen hula na fuskantar hare-hare ta sama da bindigogi da kuma yunwa yayin da bangarorin da ke fada da juna ke toshe hanyoyin shiga da kayayyakin agaji sannan farashin kaya ya yi tashin gwauron zabi.
Cibiyoyin kiwon lafiya, ciki har da na MSF da ke samun goyon bayan da suka dakatar da ayyuka, suna yawan fuskantar hari akai-akai daga sojojin RSF da ke neman a kula da lafiyarsu ko kuma su kwashe kayan abinci.
Asibitin Bashair ya yi hidima da fiye da mutane 25,000, in ji MSF, ciki har da 9,000 da suka jikkata sakamakon fashewar bama-bamai da raunukan harbin bindiga, da sauran tashe-tashen hankula.
A wata sanarwa da kungiyar ta MSF ta fitar, ta ce "Wani lokaci mutane da dama ne suka isa asibitin a lokaci guda bayan da aka yi ruwan bama-bamai ko kuma kai hare-hare ta sama kan wuraren zama da kasuwanni," inda tuni 12 daga cikinsu sun riga sun mutu.