Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya ta sanar da waɗanda suka lashe gasar karatun Alkur’ani

Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya ta sanar da waɗanda suka lashe gasar karatun Alkur’ani

Mutum 18 maza da mata da suka zama zakaru a gasar wadda aka gudanar a jihar Kebbi ne za su wakilci Nijeriya a babbar gasar da za a yi ta duniya a bana.
Majalisar ta bukaci wadanda za su wakilci kasar da su kasance jakadu nagari a duk halin da suka samu kansu yayin da suke wajen kasar. / Hoto: Others

Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA) karkashin jagorancin Sarki Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad III ta bayyana sunayen waɗanda suka lashe gasar karatun Alkur’ani wanda aka yi a jihar Kebbi a watan Disambar da ya wuce.

A wata sanarwa da Sakatare Janar na NSCIA Farfesa Is-haq Oloyede ya sanya wa hannu ta ce an karkasa gasar ne zuwa bangarori shida kuma cibiyar harkokin addinin Musulunci ta Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto ce ta shirya gasar.

Mutum 18 maza da mata da suka zama zakaru a gasar wadda aka gudanar a jihar Kebbi ne za su wakilci Nijeriya a babbar gasar da za a yi ta duniya a bana.

Sannan NSCIA ta ce cibiyar harkokin addinin Musulunci ta Jami’ar Usman Danfodiyo ce kadai aka yarda ta shirya gasar musabakar Alkur’ani a duk fadin Nijeriya.

Kuma sanawar ta bukaci wadanda za su wakilci kasar da su kasance jakadu nagari a duk halin da suka samu kansu yayin da suke wajen kasar.

TRT Afrika da abokan hulda