Kasashen Afirka sun yi maraba da yarjejeniyar Isra'ila da Hamas ta tsagaita wuta

Kasashen Afirka sun yi maraba da yarjejeniyar Isra'ila da Hamas ta tsagaita wuta

Mummunan yakin da Isra'ila ta yi a Gaza ya kashe Falasdinawa sama da 46,700 tun daga watan Oktoban 2023.
Mahmud ya jaddada muhimmancin ɗorewar tsagaita wutar, ya kuma bukaci kasashen duniya da su gaggauta kai agajin jinƙai ga al'ummar Gaza. / Hoto: AA

Ƙasashen Afirka sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza da aka cim ma tsakanin Isra'ila da Hamas, bayan shafe fiye da shekara ɗaya ana tattaunawa.

A wata sanarwa da Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta wallafa a shafin X, shugabanta Moussa Faki Mahamat ya ce: "Ina son yaba wa Qatar da Masar da Amurka kan muhimmiyar rawar da suka taka a wannan lamari."

Ya ce ƙungiyar tana kira ga a yi gaggawar aiwatar da yarjejeniyar tare da fatan a yi wa al'ummar Falasdinu adalci da tabbatar musu da zaman lafiya.

Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ma YA yaba wa kokarin Qatar, Masar, da Amurka wajen kulla yarjejeniyar.

Agajin gaggawa

Mahmud ya jaddada muhimmancin ɗorewar tsagaita wutar, ya kuma bukaci kasashen duniya da su gaggauta kai agajin jinƙai ga al'ummar Gaza.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Alhamis din da ta gabata, ya ce "Da wannan yarjejeniya, na jaddada bukatar haɗa ƙarfi da ƙarfe don daidaita yarjejeniyar tsagaita wuta tare da ba da fifiko wajen samar da agaji cikin gaggawa don rage radadin da ake fama da shi a Gaza."

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya bayyana a kafafen sada zumunta cewa, "Ina maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, bayan kwashe tsawon shekara daya ana kokarin yi, wanda Masar, Qatar da Amurka suka shirya.

Ya jaddada bukatar kai agajin jinƙai cikin gaggawa zuwa Gaza.

'Zaman lafiya mai ɗorewa'

"Wannan yarjejeniya ta nuna muhimmancin ba da agaji ga al'ummar Gaza cikin gaggawa don magance bala'in jinƙai, ba tare da wani cikas ba, har sai an samar da zaman lafiya mai dorewa ta hanyar samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu," in ji shi.

Sisi ya jaddada aniyar Masar ta tallafa wa zaman lafiya mai adalci, da kasancewa aminiyar abokiyar zaman lafiya wajen cim masa, da kare hakki na al'ummar Falasdinu.

'Zaman lafiya'

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta fitar, ta yi kira da a aiwatar da samar da zaman lafiya mai dorewa da zai tabbatar da 'yancin bil'adama na Falasdinawa da Isra'ilawa.

Ministan harkokin wajen kasar Ronald Lamola ya ce "Yarjejeniyar tsagaita wuta wani muhimmin mataki ne na farko na kawo karshen mummunan rikicin jinƙai da Falasdinawa miliyan 2.3 ke fuskanta a Zirin Gaza, wanda kotun kasa da kasa (ICJ) ta dauka a matsayin kisan kare dangi."

Sanarwar tsagaita wutar ta zo ne a rana ta 467 ta kisan kiyashin da Isra'ila ta yi wa Gaza, wanda tare da goyon bayan Amurka ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 156,000, yawancinsu mata da yara.

Yakin dai ya yi sanadin batan mutane sama da 11,000, tare da yin barna sosai da kuma rikicin jinƙai da ya lakume rayukan tsofaffi da yara da dama a daya daga cikin bala'o'in jinƙai mafi muni a duniya a 'yan kwanakin nan.

TRT Afrika