Ganau sun ce an ci gaba da yaki a Khartoum, babban birnin Sudan a ranar Laraba 19 ga watan Afrilu, duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da duka bangarori biyu masu fadan suka sanar.
Manyan kasashen duniya da suka hada da Amurka sun yi ta kokarin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin rundunar sojin kasar da kuma rundunar RSF, don a bai wa mutanen da abin ya rutsa da su damar samun kayayyakin agajin da suke tsananin bukata.
Dukkan bangarorin biyu sun amince da tsagaita wutar daga karfe 6 na kasar a ranar Talata da Laraba, amma ba a dakatar da luguden wuta ba kuma daga rundunar sojin kasar har ta RSF din sun fitar da sanarwa suna zargin juna da gaza girmama yarjejeniyar.
A kalla mutum 270 ne suka mutu tun bayan barkewar rikicin a karshen makon da ya gabata, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta kiyasta, yayin da mutum 2,600 suka jikkata.
Ga wasu jerin abubuwa da suka faru a yau Laraba
1845 GMT - WHO ta ce ma’aikatan lafiya na fuskantar hatsari
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya na yankin Ahmed al-Mandhari ya bayyana damuwarsa kan rahotannin da ke cewa an kai hare-hare kan cibiyoyin lafiya da kuma sace motocin daukar marasa lafiya a yayin da ma’aikatan lafiya ke ciki don kai majinyata asibiti.
1830 GMT – Yakin ya durkusar da fannin lafiya na Sudan
Likitoci da ma’aikatan asibiti sun bayyana irin mummunan yanayi da ake ciki na rashin ruwa da kazanta da rashin wutar da za a duba majinyata da kuma karancin abinci, lamarin da ya tursasa musu kin karbar marasa lafiya.
1809 GMT – Turkiyya na tattaunawa da dukkan bangarorin don a tsagaita wuta
Turkiyya tana tattaunawa da dukkan bangarorin biyu don a tsagaita wuta a Sudan, inda ake sa ran za a cimma yarjejeniya zuwa gobe: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Cavusoglu.
1700 GMT – Chadi ta ce ta kwace makaman sojojin Sudan a kan iyakokinta
Rundunar Sojin Chadi ta dakatar tare da kwace makaman wasu sojojin Sudan 320 wadanda suka shigar kasar a ranar Litinin, a cewar Daoud Yaya Brahim.
Brahim ya shaida wa wani taron manema labarai cewa fito na fiton da ake yi tsakanin bangarorin biyu a Sudan ka iya jawo kwararar ‘yan gudun hijira da kuma barazanar tsaro sosai.
1300 GMT - Kasashen duniya na rokon a tsagaita wuta
Ofisoshin jakadancin kasashen waje a Sudan sun yi kira ga rundunonin biyu masu fada da juna da su tsagaita wuta tare da mutunta dokokin kasa da kasa na kare fararen hula da masu ba da agaji.
Kasashen da suka yi wannan kira sun hada da Kanada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da Netherlands da Norway da Poland da Koriya ta Kudu da Spaniya da Switzerland da Sweden da Birtaniya da Amurka da kuma tawagar Kungiyar Tarayyar Turai.
1230 GMT – Uganda da Kenya na shirin kwashe ‘yan kasashensu
Kasashe da dama sun fara sanar da kwashe ‘yan kasashensu da suka makale a Sudan bayan da aka gaza tsagaita wuta.
Japan da Kenya da Uganda tuni suka sanar da fara shirin kwashe mutanensu.
1115 GMT - An ji wa wani jami'in Belgium rauni
An ji wa wani jami’in Kungiyar Tarayyar Turai dan Belgium rauni sakamakon harbin sa da aka yi da bindiga a yakin na Sudan.