Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta shawarci ‘yan ƙasar masu niyyar tafiya ƙasar Australiya su yi la’akari da “sha’anin tsaro a wasu birane” kafin su tafi.
Wata sanarwar da muƙaddashin mai magana da yawun bakin ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya fitar ta ce,”wannan na da muhimmanci ga ‘yan Nijeriya matafiya da ma ‘yan Nijeriya mazauna Australiya ne saboda rahotannin wariya da tsangwama da kuma zagi da ake yi wa baƙi.”
Sanarwar ta fito ne bayan gwamnatin Australiya ta shawarci ‘yan ƙasarta masu niyyar zuwa Nijeriya su sake tunani.
Ranar Talata ne dai ma'aikatar harkokin wajen Australiya ta shawarci 'yan Australiya su sake tunani kan zuwa Nijeriya domin rashin tabbas na tsaro da kuma barazanar harin ta'addanci da garkuwa da mutane.
Bayan wannan ne ma'aikatar harkokin wajen Nijeriya ta fitar da nata shawarar ga 'yan Nijeriya.
“Ƙarin yawan laifukan ƙin jinin Yahudawa da Larabawa da kuma ƙin jinin Musulmai a Australiya ya ƙara barazanar kai farmaki, dalilin da ya sa ake buƙatar yin taka-tsan-tsan,” in ji ma’aikatar hakokin wajen Nijeriya.
Ebienfa ya ce duk da cewa Australiya ta kasance ƙasa mai maraba da al’adu da haƙuri a baya, an samu laifukan ƙin jinin Musulmai da Yahudawa a wasu biranen ƙasar.
“A farkon watan Disambar shekarar 2024, wani abu mai sosa rai ya faru a wata unguwa da ke gefen Sydney, inda aka ƙona wata mota kuma aka yi rubutun ƙin jinin Isra’ila a jikin bangon wasu gine-gnie da ke kusa,” a cewar ma’akatar harkokin wajen Nijeriya.
Ma’aikatar ta nemi duk matafiya ‘yan Nijeriya da ke zama a Australiya da aka musgunawa su tuntuɓi ofishin jakadancin ƙasar da ke Canberra, babban birnin ƙasar Australiya.