Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Sudan ya ce ba zai yiwu ba rundunar RSF ta koma matsayin da take kafin a fara yaƙi.
Abdel Fattah al-Burhan ya yi wannan kalaman ne ranar Talata a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na ƙasar Sudan domin murnar cika shekara 69 da samun ‘yancin kan ƙasar daga Birtaniya.
Sai dai kuma ya bayyana cewa zai "shiga duk wani shiri da zai kawo ƙarshen yaƙin tare da tabbatar da dawowar fararen-hula gidanjensu cikin aminci."
"Yanayin ba zai koma yadda yake kafin ranar 15 ga watan Afrilu 2023 ba kuma ba za mu yarda da kasancewar waɗannan masu kisan kai da laifuka da magoya bayansu a cikin al'ummar Sudan ba," a cewar Burhan a lokacin da yake magana kan RSF.
Ya ƙara da cewa mayaƙan RSF suna gana wa mutanen Sudan uƙubar kisa da yunwa da kuma gudun hijira.
Yaƙin basasar Sudan
Kimanin mutane 25,000 ne aka kashe kuma aka raba miliyan goma da gidajensu tun watan Afrilun shekarar 2023 a lokacin da aka fara yaƙin neman iko tsakanin sojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da rundunar RSF ƙarƙashin mataimakinsa a wancan lokacin, Mohamed Hamdan Dagalo.
Yaƙin ya watsu zuwa jihohi 13 cikin 18 na ƙasar Sudan, lamarin da ya janyo bala’in lalata abubuwa da kuma tura miliyoyin mutane cikin yunwa da mutuwa.
Jerin ƙoƙarin shiga-tsakani da wasu ƙasashe suka jagoranta ciki har da Amurka da Saudiyya bai yi nasarar tabbatar da tsagaita wuta ba tukunna yayin da ɓangarorin sojin Sudan da RSF ke zargin juna da yi wa yunƙurin sulhu zagon ƙasa.